An Tsare Tsohon Gwamna a Kotu a Dalilin ‘Bashin’ Naira Miliyan 900 da ake bin Shi
- Owoseni Ajayi ya yi karar Ayodele Peter Fayose a babban kotun jihar Ekiti mai zama a garin Ado-Ekiti
- Lauyan yace akwai wasu miliyoyin da yake bin Tsohon gwamnan na jihar Ekiti bashi da ba a biya shi ba
- ‘Dan siyasar ya sanar da Alkali ayi watsi da karar, amma ya yarda ya san wanda ya shigar da shi kuliya
Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose ya samu kan shi a gaban Alkali a wani babban kotun jiha da ke zama a garin Ado Ekiti.
The Nation ta kawo rahoto a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba 2022 cewa an yi karar Ayodele Peter Fayose saboda ya gaza biyan bashin N900m.
Tsohon kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati a lokacin mulkin Fayose, Owoseni Ajayi shi ne ya kai karar tsohon mai gidansa a kotu.
Owoseni Ajayi wanda ya yi Kwamishinan shari’a tsakanin 2003 da 2006 da kuma 2014 zuwa 2017 ya yi da’awar yana bin tsohon gwamnan bashin kudi.
Ajayi ya tsayawa Fayose a shari'a 18
An rahoto Ajayi yana cewa kamfaninsa ya yi wa Ayo Fayose aiki, ya kare shi a shari’a 18 da aka yi da nufin zai karbi N50m, amma ba a biya sa kudin ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda ya yi korafi, a shari’ar da ya shigar mai lamba HAD/113/2018, Lauyan yace ya tsayawa Mista Fayose a lokacin da aka tunbuke shi a 2016.
Lauyan ya kuma fadawa kotu cewa ya wanke tsohon gwamnan a shari’ar da aka rika yi tsakaninsa da hukumar EFCC, kuma ba a biya shi kudin aiki ba.
Jaridar Sun tace Lauyan ya roki Alkali ya tursasa Fayose ya biya wadannan kudi da gaggawa.
Ruwa ya shiga cikin bashi
Ajayi ya nemi kotu ta sa tsohon gwamnan ya biya karin ruwa na 20% daga 2018 da 10% daga lokacin da aka yanke hukunci saboda dadewar bashin.
Jagoran na jam’iyyar PDP ya bukaci Mai shari’a Olukayode Ogundana ya yi watsi da wannan shari'a da cewa Lauyoyi ba su shigar da karar da kyau ba.
Fayose ya fadawa Ogundana ya san wanda ya shigar da karar, kuma ya yi masa aiki tsakanin 2016 da 2017. A karshe an daga shari’ar sai 13 ga Disamba.
Sarakunan Anambra za su yi PDP?
An samu rahoto Mai martaba Igwe Chuma Agbala da Nick Obi sun fitar da jawabi a madadin Sarakunan Idemili domin karyata goyon bayansu ga PDP.
Masu sarautar sun ce basu da gwani tsakanin Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da sauran 'yan takaran da za su shiga zabe.
Asali: Legit.ng