2023: Gaskiyar Abun da Ke Tsakanina Da Wike, Ortom da Sauran Jiga-Jigan PDP, Peter Obi Ya Fasa Kwai

2023: Gaskiyar Abun da Ke Tsakanina Da Wike, Ortom da Sauran Jiga-Jigan PDP, Peter Obi Ya Fasa Kwai

  • Gabannin zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ya fadi abun da ke tsakaninsa da Wike da sauran gwamnonin PDP hudu
  • Obi ya bayyana cewa sun yi hadaka da gwamnonin ne saboda ra'ayinsu na kishin Najeriya da son inganta kasar
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom

Benue - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ya yi bayani kan gaskiyar alakar da ke tsakaninsa da wasu fusatattun gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Obi ya ce yarjeniniya guda da ke tsakaninsa da gwamnonin na PDP ya kasance a kan ra'ayinsu na son mayar da Najeriya kasa mai inganci.

Ya yi bayanin ne a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, yayin da yake jawabi a Makurdi a wata ziyara da ya kaiwa gwanan jihar Benue, Samuel Ortom, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Rikicin PDP Ya Kara Dagulewa, Shugaban Jam'iyyar Ya Yi Fatali da Shawarin Dattawa

Peter Obi, Wike da Ortom
2023: Gaskiyar Abun da Ke Tsakanina Da Wike, Ortom da Sauran Jiga-Jigan PDP, Peter Obi Ya Fasa Kwai Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter
Abu guda da ke tsakanina da su shine suna da kishin Najeriya," inji Obi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake yabama Gwamna Ortom kan yadda ya tunkari matsalar rashin tsaro a jihar Benue, Obi ya soki gwamnatin APC kan nuna rashin shugabanci da halin ko'in-kula ga mutane a lokacin rikici, rahoton Channels TV.

A nasa bangaren, Ortom ya shawarci Obi da ya tattauna da sauran manyan yan takarar shugaban kasa tare da jajircewa don yiwa mutane hidima.

Gwamnan ya ce da ace shi ba dan PDP bane, da ya yiwa dan takarar na LP aiki.

Wasu daga cikin fusatattun gwamnonin PDP sun hada da Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Mista Ortom.

Ku tuna cewa gwamnonin aun nemi shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu yayi murabus don wani dan kudu ya dare kujerar.

Kara karanta wannan

2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

Ana ganin wasu daga cikin gwamnonin na PDP za su marawa Peter Obi baya a zaben shugaban kasa na 2023.

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

A wani labarin, ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya ce addu'a Najeriya ke bukata daga gwamnatin Amurka maimakon gargaji wanda ya jefa mutane cikin rudani.

Ministan ya bayyana cewa gargadin da Amurka tayi kan yuwuwar kai harin ta'addanci a Abuja ya jefa jama'a cikin tsoro sannan ya razanar da yan Najeriya ta yadda har sun gaza daukar matakin da ya dace, rahoton Vanguard.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa barazanar bai yi tsanani ba, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnati na kan lamarin da taimakon hukumomin tsaro da na leken asiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng