2023: Ɗan Takarar Gwamna Ya Nemi Jam'iyyar PDP Ta Kori Wike Kan Abu Daya
- Jigon PDP da ya nemi takarar gwamna a Delta, Barista Odebala, ya nemi uwar jam'iyya ta sallami gwamna Wike na jihar Ribas
- Mista Odebala yace gwamnan kokarinsa ya tarwatsa jam'iyyar PDP kuma hakan babban abun kunya ne ga jam'iyyar
- A wani bidiyo ya yi kira ga uwar jam'iyya ta ƙasa karkashin Dakta Ayu ta rubuta masa takardar kora
Delta - Wani ɗan takarar gwamna da ya nemi tikitin jam'iyyar PDP a jihar Delta, Barista Ejaife Omizu Odebala, ya bukati a kori gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kan abinda ya kira cin amana.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa a wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, Odebala, ya zargi Wike da cin dunduniyar jam'iyyar PDP wanda hakan ya fara durƙusad da ita.
Yace Wike ya zama fitini kuma abun kunya ga babbar jam'iyyar adawa bisa haka ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su gaggauta tattara masa komatsansa ya bar PDP.
A kalamansa, Barista Odebala ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sunana Honorabul Barista Ejaife Omizu Odebala, mamba a jam'iyyar PDP; Gwamna Wike wanda mamba ne a jam'iyyarmu ya jima yana kokarin tarwatsa jam'iyyar, bisa haka hasken PDP ke dusashewa a hankali."
"Wike ba shi da niyyar ci gaba da ba PDP haɗin kai, don haka ina rokon uwar jam'iyya ta ƙasa karƙashin jagorancin Dakta Iyirchia Ayu ta gaggauta korar Wike daga PDP cikin gaggawa."
"Ya zama ƙarfen ƙafa kuma yana jawo wa jam'iyya babban abun kunya a idon duniya, ba zai yuwu mutum ɗaya ya hana jam'iyya rawar gaban hantsi ba domin ɗaukar fansa."
Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa har yanzun babu zaman lafiya a PDP sakamakon ɓallewar gwamna Wike, wanda ya bukaci Ayu ya yi murabus.
Gwamnan wanda ke da goyon bayan wasu gwamnonin PDP huɗu, ya yi ikirarin cewa Ayu ya ɗauki alƙawarin sauka daga shugabancin PDP idan har tikitin shugaban ƙasa ya tafi yankin arewa.
Atiku ya tafi Amurka
A wani labarin kuma Atiku Ya Dira Kasar Amurka Domin Zawarcin Manyan Jami'ai Kan Burinsa Na 2023
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, na ƙasar Amurka tun ranar Talata.
Tsohon mataimakin shugaban zai gana da wasu Jami'an gwamnatin Biden domin neman goyon bayansu a 2023.
Asali: Legit.ng