2023: Abinda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Tambayi Kowane Mai Burin Gaje Buhari, Dattawan Arewa

2023: Abinda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Tambayi Kowane Mai Burin Gaje Buhari, Dattawan Arewa

  • Dattawan arewa sun shawarci yan Najeriya da su bincika tare da latsa dukkan masu son darewa kujerar shugaban kasa a 2023
  • Mai magana da yawun NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce akwai bukatar al'ummar kasar su tambayi yan takarar kan yadda za su magance matsalolin kasar idan aka zabe su
  • Sun kuma yi kira ga takwarorinsu na sauran yankunan kasar a kan su kwaikwayi abun da suka yi na kiran yan takarar don su baje masu kolin monufofinsu

Kungiyar dattawan arewa ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su tambayi yan takarar shugaban kasa kan yadda zasu magance matsalolin kasar idan aka zabe su.

Kakakin kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana haka yayin da ya fito a shirin Sunday Politics na Channels TV.

Hakeem Baba-Ahmed
2023: Abinda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Tambayi Kowane Mai Burin Gaje Buhari, Dattawan Arewa Hoto: guardian.ng
Asali: Twitter

Ya ce:

“Akwai bukatar yan Najeriya su latsa yan takararmu. Ya kamata mu gano wa za mu yarda da shi a cikin wadannan mutane.”

Kara karanta wannan

Yadda Mutum 306 Suka Samu Tagomashi Daga Kudin Zakkah, An Raba Masu N55m

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da manyan yan takara da suka hada da Peter Obi na LP, Atiku Abubakar na PDP, Bola Tinubu na APC da Rabiu Kwankwaso na NNPP ke da tarin kwarewa, ya ce ya kamata su nunawa ‘yan Najeriya hanyar da za su bi don shawo kan manyan matsalolin kasar, rahoton Daily Post.

Baba-Ahmed ya kara da cewa:

“Wadannan mutane ne masu tarin kwarewa a fannin shugabantar mutane. Wadannan mutane ne masu nauyin aljihu tunda har suka kai matakin da suke yanzu na yan takara. Yakamata a binciki halayyarsu.”

Ya ce taron da kungiyar ta kira kwanaki don ba yan takarar damar fadawa yankin arewa da yan Najeriya tanadin da suka yi masu ne idan aka zabe su a 2023.

A cewarsa, ya kamata sauran yankuna su yi koyi da irin wannan tattaunawar don yan Najeriya su samu damar yin zabi nagari a shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Tayi Nasarar Daure 'Yan Damfara 2, 800 a Watanni 10 a 2022

“Idan za a iya maimaita shi a sauran hanyoyi, ya kamata ayi hakan. Akwai bukatar a latsa wadannan yan takara kai tsaya su fadi abun da suke son yi."

Ya ce kungiyar za ta yi nazari kan manufofin yan takarar domin ba ‘ya’yanta karin haske kan abun da za su iya yi.

Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

A wani labarin, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya magantu a kan yiwuwar hadakarsu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso gabannin zaben 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa Shettima ya bayyana cewa shi da kansa zai nemi Kwankwaso a daidai lokacin da ya kamata.

Tsohon gwamnan na jihar Borno wanda ke gabatar da jawabi a taron kungiyar limaman birnin tarayya Abuja, yana barkwanci ne da tsohon dan majalisar wakilai, Garba Ibrahim Muhammed, wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a taron.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za su iya faruwa idan CBN ya buga sababbin N200, N500 da N1000

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng