Tinubu: Abin da Buhari Ya Fada Mani Yayin da Na Nemi Ya Zakulo Mani Mataimakina

Tinubu: Abin da Buhari Ya Fada Mani Yayin da Na Nemi Ya Zakulo Mani Mataimakina

  • Asiwaju Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ya shiga rudani a lokacin tsaida ‘dan takaran shugaban kasa
  • ‘Dan takaran na APC yace Muhammadu Buhari ya tsaya masa, kuma yace ya dauki duk wanda yake so
  • Tinubu yace Gwamnonin Arewa sun taimaka masa, suka goyi bayan ya samu tikitin takara a zaben 2023

Ondo - Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, ya bada labarin yadda ya yi da shugaban kasa a kan takara.

A ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba 2022, Daily Trust ta rahoto Asiwaju Bola Tinubu yana cewa ya nemi shugaban kasa ya zama masa abokin takararsa.

‘Dan takaran shugabancin kasar ya yi wannan bayani ne a sa'ilin da ya ziyarci gidan jagoran kungiyar Afenifere, Pa Reuben Fasoranti jiya a garin Akure.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Babbar Kungiyar Yarbawa da Gwamnan PDP

Bola Tinubu wanda yake rike da tutar APC a babban zabe mai zuwa yace shugaban kasa ya jajirce wajen ganin ya samu takara yayin da ya fuskanci adawa.

Na shiga cikin rudani - Tinubu

Punch ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa ya samu kan shi a cikin rudani a gabar zaben fitar da gwani, amma gwamnonin Arewa suka mara masa baya a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Arewa sun nuna hadin-kan Najeriya. Wasu sun nemi shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da wani ‘dan takara, amma yace a’a, dole a bi tsarin siyasa.
Bola Tinubu
Bola Tinubu a Kaduna Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook
Shugaban kasa yace duk wanda ya jagwalgwala tsarin jam’iyyar APC, zai gamu da fushinsa.
A karshe gwamnonin APC suka ce dole mulki ya koma Kudu, musamman kudu maso yamma.
Gwamnoni irinsu Malam Nasir El-Rufai da Abdullahi Umar Ganduje da sauransu, suka goyi baya na.

- Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Ka yi kadan: Gwamna Wike Ya Aikawa Shugaban Jam’iyyar PDP Sabon Raddi

‘Dan takarar Mataimakin shugaban kasa

"Shugaban kasa yace yana na cancanta in yi mulki. Lokacin da na nemi ya zabo mani ‘dan takarar mataimaki, sai yace mani in zabi duk wanda nake so.
Wannan ya sa na dauko wanda ya cancanta, Kashim Shettima, wanda bai taba fadi zabe ba. Na zabe shi ne saboda yadda yak are kiristoci a jiharsa.

- Bola Tinubu

Peter Obi ya ga samu, ya ga rashi

An samu rahoto jagororin Afenifere sun warware mubaya’ar da Shugabansu ya yi wa Peter Obi, sun ce Bola Ahmed Tinubu ne wanda za a zaba a 2023

Dattawan Yarbawa daga jihohin Legas, Oyo, Ogun, Ondo, Osun, Ekiti har da Kwara da Kogi za su goyi bayan APC ne a zaben shuagaban kasa da za ayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng