Jigon NNPP Ya Yi Hasahen Faduwar Tinubu da Atiku a Zaben 2023

Jigon NNPP Ya Yi Hasahen Faduwar Tinubu da Atiku a Zaben 2023

  • Jigon jam'iyyar NNPP mai kayan dadi ya yi hasashen cewa Kwankwaso zai lallasa Tinubu da Atiku ya gaji shugaba Buhari a 2023
  • Alhaji Tijjani yace tsohon gwamnan Kano ya banbanta da sauran yan takara domin ya yi an gani a wasu jihohi
  • Ya kuma bayyana cewa APC da PDP sun gaza, ba su da idom da zasu kalli yan Najeriya a zaɓe mai zuwa

Kaduna - Wani jigon jam'iyya mai kayan marmari NNPP, Alhaji Ahmed Tijjani, yace ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Kwankwaso, zai lallasa sauran yan takara ya ci zaben 2023 mai zuwa.

Tijjani ya yi wannan hasashen ne yayin wata zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Kaduna ranar Lahadi.

Rabiu Musa Kwankwaso.
Jigon NNPP Ya Yi Hasahen Faduwar Tinubu da Atiku a Zaben 2023 Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Twitter

A rahoton da Vanguard ta tattara, Ahmed Tijjani, yace:

Kara karanta wannan

2023: Tsagin Gwamna Wike Sun Sake Yunkuro Wa, Sun Huro Sabuwar Wuta a Jam'iyyar PDP

"Abinda NNPP ta iya cimmawa cikin watanni uku kacal da kirkirota da mata rijista, jam'iyyun APC da PDP ba zasu iya cimma wurin ba a tsawon shekara."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan ka duba yaddda mutane suka rungumi NNPP zaka gane cewa ba abinda zai dakatar da mu daga lashe zaɓen 2023. Ku duba yadda mutane ke tarban Kwankwaso duk jihar da ya kai ziyara tun kafin kamfe."
"Ina tunanin wannan alama ce da ta fito fili domin mutane su shaida cewa muna kan hanyar lashe zaɓen shugaban ƙasan da ke tafe."

Kwankwaso ba ɗaya yake da sauran ba - Tijjani

Tijjani ya ƙara da cewa saɓanin sauran yan takara, Kwankwaso tattare yake da nasarorin a zo a gani da zai alfahari da su, waɗanda ya gudanar a lokacin yana rike da wasu kujerun siyasa a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

"Mu duba yan takara huɗu da ke neman shugaban kasa a 2023, Tinubu zai faɗa muku ku zaɓe ni zan muku kaza da kaza, haka Atiku, Peter Obi kuma kowa ya san ɗan takarar Soshiyal Midiya ne."
"Amma NNPP zata gaya wa yan Najeriya cewa Kwankwaso ya yi kaza da kaza a Kano da wasu jihohin ƙasar nan, idan kuka amince masa a 2023 zai maimaita haka harda kari a matakin ƙasa."

A cewarsa, APC da PDP sun kunyata 'yan Najeriya ta kowane fanni don haka akwai bukatar sabuwar jam'iyya ta karɓi jagorancin Najeriya.

A wani labarin kuma Tinubu ya gamu da cikas yayin da Mambobin APC Sama da 200 Suka koma PDP a Yankin Wani Gwamnan Arewa

Gabannin zaben 2023, jam'iyyar APC ta rasa daruruwan mambobinta a yankin Kofar Kola da ke Birnin Kebbi, babbar birnin jihar Kebbi.

Masu sauya shekar da suka hada da maza 134 da mata 84 sun koma jam'iyyar PDP mai adawa a kasar.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Buhari Ya Kiyaye, ‘Yan APC Dinsa Na Neman Bata Masa Suna a Ofis

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262