Atiku, Tinubu, Peter Obi: Yadda PDP, APC Da Labour Party Za Su Raba Ƙuri'un Kudu Maso Yamma Ya Bayyana

Atiku, Tinubu, Peter Obi: Yadda PDP, APC Da Labour Party Za Su Raba Ƙuri'un Kudu Maso Yamma Ya Bayyana

  • Dele Momodu, ya ce Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Bola Tinubu na APC ne za su raba kuri'un yankin kudu maso yamma
  • Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar na PDP ya ce a Legas ne kawai za a raba kuri'un da dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi
  • A cewar Momodu, Atiku ya fi Peter Obi da Bola Tinubu damar samun kuri'u a kudancin Najeriya

Daya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi fashin baki kan kuri'un da jam'iyyu za su iya samu a kudu maso yamma.

A hirar da ya yi da Nigerian Tribune, gogaggen dan jaridar ya ce a jihar Legas ne kadai yan takarar 3 za su raba kuri'u cikin jihohin kudu maso yamma.

Kara karanta wannan

2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

Obi, Atiku, Tinubu
Atiku, Tinubu, Peter Obi: Yadda PDP, APC Da LP Za Su Raba Kuri'un Kudu Maso Yamma ya Bayyana. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Momodu, yan takarar da ke kan gaba sune Bola Tinubu na jam'iyyar APC, Peter Obi na Labour Party, LP, da Atiku Abubakar na PDP.

Jigon na PDP ya jadada cewa Obi ba shi da yan siyasa na kusa da talakawa da za su tattaro masa kuri'u, ko da a kudu maso gabas, ba bu alamun zai samu kuri'u da yawa a zaben 2023.

Shin Atiku zai iya cin zabe a kudu maso gabas a 2023?

Ya dage cewa Atiku ya kashe tsintsu daya da dutse daya ta hanyar zaben mutumin Delta Ibo a matsayin abokin takara, Ifeanyi Okowa, hakan na nufin dan takarar shugaban kasar na PDP bai ware Ibo ba, duk da cewa mataimakinsa daga kudu maso kudu ya fito.

Da ya ke magana da yiwuwar samun nasarar Atiku a kudu maso yamma, Momodu ya ce fafatawa za a yi tsakanin Tinubu na APC da Atiku na PDP.

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hattara Da Mayaudaran Ƴan Siyasa", APC Ta Aikewa Ƴan Najeriya Sako Mai Ƙarfi A Gabanin Zaɓen 2023

Wani sashi na jawabinsa na cewa:

"Idan muka bar Legas, muka tafi Oyo, Ogun, Osun, Ekiti da Ondo; a wadannan wuraren fafatawa za a yi tsakanin Atiku da Tinubu. Babu tantama kan hakan. Hakan, na fada maka cewa a Kudu a halin yanzu, Atiku fi Tinubu da Obi damar samun nasara a Arewa."

Hantar Peter Obi Ta Kaɗa A Yayin Da Tinubu Ya Samu Gagarumin Gudunmawa Daga Babban Jigo A Yankin Ibo

Bayan bada gidansa a matsayin ofishin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, tsohon shugaban jam'iyyar APC a jihar Enugu, Dr Ben Nwoye, ya dauki wani mataki don jam'iyyar ta yi nasara.

Hakan na zuwa ne a yayin da ya bada gudumawar motoccin yakin neman zabe dauke da hotunan Tinubu/Shettima don bunkasa kamfen din shugaban kasa gabanin zaben 2023, The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel