Hantar Peter Obi Ta Kaɗa A Yayin Da Tinubu Ya Samu Gagarumin Gudunmawa Daga Babban Jigo A Yankin Ibo

Hantar Peter Obi Ta Kaɗa A Yayin Da Tinubu Ya Samu Gagarumin Gudunmawa Daga Babban Jigo A Yankin Ibo

  • Takarar shugabancin kasar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sake samun babban tagomashi a siyasance
  • Gabanin babban zaben shekarar 2023, a jigo a jam'iyyar APC a jihar Enugu ya bada tallafin motocci da allunan talla ga Tinubu a jihar
  • Dr Ben Nwoye ya bada wannan gaggarumin gudunmawar ne watanni kadan bayan ya bada gidansa a matsayin ofishin kamfen na Tinubu/Shettima

Enugu - Bayan bada gidansa a matsayin ofishin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, tsohon shugaban jam'iyyar APC a jihar Enugu, Dr Ben Nwoye, ya dauki wani mataki don jam'iyyar ta yi nasara.

Hakan na zuwa ne a yayin da ya bada gudumawar motoccin yakin neman zabe dauke da hotunan Tinubu/Shettima don bunkasa kamfen din shugaban kasa gabanin zaben 2023, The Nation ta rahoto.

Motoccin kamfen
Hantar Peter Obi Ta Kada A Yayin Da Tinubu Ya Samu Babban Kyauta Daga Fitaccen Jigo A Yankin Igbo. Photo credit: Tinubu Support Group.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ba Wa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa

Nwoye ya bada dalilin yin wannan gudunmawar

Nwoye ya kuma kafa allunan talla da dama da ya dauki nauyin a haska hotunan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jihar Enugu, kasa da watanni uku bayan bada gidansa a matsayin ofishin kamfen.

Legit.ng ta tattaro cewa an kafa allunan talla na Tinubu/Shettima a wasu muhimman wurare a jihar.

Da ya ke magana da manema labarai a Enugu a ranar Juma'a, 28 ga watan Oktoba, a kan gudunmawar, jigon na APC wanda kuma tsohon kwamishina ne na kudu maso gabas a Ma'aikatar FCCPC ya ce:

"Na yi hakan ne saboda imani cewa Ahmed Bola Tinubu da abokin takararsa Kashim Shettima sune yan takara mafi cancanta a cikin wadanda ke takarar zaben 2023.
"Ba tare da yin alfahari ba, Mai girma, Sanata Ahmed Bola Tinubu, da abokin takararsa, Mai girma Kashim Shettima, shugabanni ne sanannu ne kuma an gwada su an amince da su za su iya kai Najeriya ga tudun na tsira."

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hattara Da Mayaudaran Ƴan Siyasa", APC Ta Aikewa Ƴan Najeriya Sako Mai Ƙarfi A Gabanin Zaɓen 2023

2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya yi alkawarin tattaro kan masu zabe a Akwa Ibom da wasu wuraren don ganin nasarar dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu.

Akpabio, wanda shine dan takarar sanata na Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, ya ce tabbatar da cewa Tinubu ya zama shugaban kasa na gaba aiki ne da ya zama dole a aiwatar saboda tsaro da cigaban Najeriya, The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164