Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Na PDP Ya Rasa Magoya Bayansa Fiye Da 5,000, Sun Koma APC
- Abdulazeez Adediran, (Jandor), dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Legas, ya rasa magoya bayansa masu yawa bayan sun koma APC
- Dr Obafemi Hamzat, mataimakin gwamnan jihar Legas na cikin jiga-jigan APC da suka tarbi masu sauya shekar a sakatariyar APC
- Wadanda suka sauya shekar da aka ce sun dara 5000 sun bayyana cewa Jandor baya tafiya tare da su don haka suka sauya shawarar komawa APC da wasu dalilan
Jihar Legas - Dumbin magoya bayan dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Legas, Abdulazeez Adediran da aka fi sani da Jandor, a ranar Alhamis, sun koma jam'iyyar APC.
Wadanda suka sauya shekan mambobin kungiyar Lagos4Lagos wanda Jandor ya kafa, rahoton Daily Trust.
An ce wadanda suka sauya shekar sun fi 5000 tare da shugabanninsu a kananan hukumomi da dama a jihar.
An tarbe su a hukumance a wani taro da aka yi a sakatariyar APC da ke Acme road.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tsaffin magoya bayan Jandor din sun mika duk wani kayayyakinsa da ke hannunsu a wurin taron.
Mataimakin gwamnan jihar Legas, Dr Obafemi Hamzat da wasu jiga-jigan jam'iyyar sun halarci a taron.
Wasu daga cikin wadanda suka sauya shekar zuwa APC sun bayyana dalilansu
Wasu daga cikin wadanda suka sauya shekar sun ce ba za su iya yarda da Jandor ba wanda suka ce baya tafiya tare da su.
Sun bayyana cikakken goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas a zaben 2023.
Jagoran masu sauya shekan, Hon. Idowu Daramola daga Mushin, Ilupeju Ward 1 ya ce nasarar Tinubu yasa sun sake shawara.
Wani jagora cikin wadanda suka dawo APC din, Mr Ahmed Mofeola, ya ce Tinubu ya tabuka abin azo a gani a kasar kuma lokaci ya yi da za a saka masa ta hanyar zabensa.
Ya ce:
"Kuri'a ta ta Tinubu da Sanwo-Olu ne."
'Rabon Shinkafa' Ba Karfafawa Matasa Gwiwa Bane, Shahararren Gwamnan Najeriya Ya Faɗa Wa Ƴan Siyasa
A wani rahoton, gwamnanZaben 202 ya bayyana ayyukan tallafi da wasu yan siyasa a jihar ke yi a matsayin 'sadaka ga mabukata'.
A cewar Soludo, rabawa matasa buhunan shinkafa ba karfafawa bane, kawai dai sadaka ne na kayan abinci, rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng