Gwamnonin Jam'iyyar APC Biyu Sun Ziyarci Gwamna Wike Na Jihar Ribas
- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da takwaransa Ben Ayade na Kuros Riba sun ziyarci gwamna Wike a Patakwal
- Gwamnonin biyu sun yi nasarar hawa kujerar mulki a karkashin PDP amma daga bisani suka sauya sheka zuwa APC
- Bayanai sun nuna cewa sun isa gidan Wike da daren Laraba tare da rakiyar gwamnan Abiya daga nan suka shiga ganawa a sirrance
Rivers - Mutum biyu da ba'a tsammanin kai ziyararsu, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da takwaransa gwamna Ben Ayade na jihar Cross River, yanzu haka suna Patakwal, babban birnin jihar Ribas.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnoninn biyu sun kai ziyara ne a matsayin bakin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, jihar dake yankin Neja Delta.
Tun asali dai gwamna Umahi da Gwamna Ayade sun ɗare kan madafun iko ne karkashin inuwar jam'iyyar PDP amma daga bisani suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan.
Bayanai sun nuna cewa an hangi gwamnonin da daren Laraba a Rumuekirikom, ƙaramar hukumar Obio Akpor, a gidan Wike na ƙashin kansa tare da rakiyar takwaransu na jihar Abiya, Okezie Ikpeazu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ta gano cewa gwamnonin sun shiga ganawar sirri wanda har kawo yanzu babu cikakken bayani kan abinda suka tattauna.
Wannan na zuwa ne makonni bayan gwamna Wike ya gaya wa duniya cewa ba zai yi wa Atiku Abubakar, yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ba.
A cewarsa, ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya karkashin inuwar PDP ya zaɓi makiyar jihar Ribas, ya snaya su a tawagar kamfe ɗinsa.
Gwamnan Ribas da wasu gwamnoni hudu dake mara masa baya sun kafe kan cewa har sai an biya musu bukatarsu ta sauke shugaban PDP na ƙasa kafin su haɗe da Atiku.
Jam'iyyar PDP ta yi rashin jiga-jigai a jihar Sokoto
A wnai labarin kuma Hadimin Tambuwal, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Dandazon Mambobi Sun Koma APC
Kusan wata ɗaya bayan fara kamfen 2023, jam'iyyar APC ta kara samun gagarumin goyon baya a jihar Sakkwato.
Hadimin gwamna Aminu Tambuwal da mataimakin shugaban PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da magoya bayansu.
Asali: Legit.ng