Jam'iyyar APC Ta Sake Karban Jiga-Jigan PDP Da Suka Sauya Sheka a Sokoto

Jam'iyyar APC Ta Sake Karban Jiga-Jigan PDP Da Suka Sauya Sheka a Sokoto

  • Jam'iyyar APC ta sake samun karin goyon baya yayin da wasu mambobin PDP suka sauya sheka daga PDP a Sakkwato
  • Sanata Aliyu Wamakko ta bakin kakakinsa, Bashar Abubakar, yace PDP mai mulkin jihar na gab da zama tarihi
  • Wasu jiga-jigan PDP ciki har da Sakataren shiyya, Alhaji Musa, sun bar tafiyar su Tambuwal sun koma APC

Sokoto - Jam'iyyar The All Progressives Congress, (APC) reshen jihar Sakkwato tace ta sake karɓan sabon rukunin masu sauya sheka daga jam'iyyar PDP gabanin babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Bashar Abubakar, kakakin Sanata Aliyu Wamakko, ya raba wa manema labarai ranar Talata a birnin Sakkwato.

Jam'iyyar APC.
Jam'iyyar APC Ta Sake Karban Jiga-Jigan PDP Da Suka Sauya Sheka a Sokoto Hoto: dailynigerian
Asali: UGC

A cewar Abubakar, masu sauya sheƙar sun fito ne daga ƙaramar hukumar Sabon Birni, kuma cikinsu har Sakataren jam'iyyar PDP na shiyya, Alhaji Musa da wasu shugabanni a matakin gunduma.

Kara karanta wannan

APC Ta Dakatar Da Tsohon Dan Majalisar Tarayya Da Tsohon Kwamishina

Yace sabbin mambobin jam'iyyar APC sun samu kyakkyawar tarba a wani ɗan kwaryakwaryan taro da aka shirya a garin Sabon Birni, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idris Gobir, abokin takarar ɗan takarar gwamnan jihar Sakkwato karkashin inuwar APC, Ahmad Aliyu, ne ya karɓi masu sauya shekar hannu biyu a wurin taron.

Abubakar yace, "Tururuwar mutanen da ake samu suna sauya sheka (zuwa APC) wata babbar alama ce da ke nuna jam'iyya mai mulkin jihar ta zama tarihi."

Ya ƙara da jaddada kudirin jam'iyyar APC na samar da walwala da jawo kowa a jiki tare da yin aiki da gudummuwar kowane mamba domin cika muradan al'ummar Sokoto.

Meyasa jiga-jigan suka zaɓi komawa APC?

Masu shekar sun bayyana cewa sun zaɓi rungumar APC ne domin su ba da tasu gudummuwar wajen fafutukar samun nasara a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Ayyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC Na Wata Jiha a 2023

A wani labarin kuma tsohon Ministan Sufuri ya bayyana dalilin da yasa shi da wasu gwamnonin PDP suka koma APC a baya

Daraktan midiya na tawagar kamfen Tinubu, Femi Fani Kayode, yace ya zaɓi komawa APC ne saboda abinda yake tsoro ya kauce a jam'iyyar.

Tsohon ministan yace sheɗanun da suka dabaibaiye APC sun yi ƙaura zuwa PDP, shiyasa shi da wasu gwamnoni suka fita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel