2023: Ɗaliban Najeriya Sun Goyi Bayan Takarar Tinubu Da Shettima, Sun Bada Ƙwakwarar Dalili

2023: Ɗaliban Najeriya Sun Goyi Bayan Takarar Tinubu Da Shettima, Sun Bada Ƙwakwarar Dalili

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya samu babban tagomashi a siyasarsa
  • Hakan na zuwa ne a yayin da daliban Najeriya suka bayyana goyon bayansu ga takarar shugaban kasa na Tinubu/Shettima, watanni kafin zaben 2023
  • Sunday Asefon, jagoran, kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard, ya sha alwashin hada kan daliban Najeriya don zaben mutanen biyu a zaben na 2023

Shugaban kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard na kasa, Mr Sunday Asefon, a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba, a Abuja, ya yi alkawarin tattaro kan daliban Najeriya zu zabi Tinubu Shetima a zaben shugaban kasa na 2023.

Asefon ya yi wannan alkawarin ne yayin kaddamar da kungiyar Tinubu/Shettima Vanguards, The Nation ta rahoto.

Tinubu da Shettima
2023: Daliban Najeriya Sun Goyi Bayan Tinubu Da Shettima, Sun Bada Kwakwarar Dalili. Hoto: @OfficialBAT
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hattara Da Mayaudaran Ƴan Siyasa", APC Ta Aikewa Ƴan Najeriya Sako Mai Ƙarfi A Gabanin Zaɓen 2023

Asefon, tsohon shugaba na kasa na kungiyar daliban Najeriya, (NANS), ya ce kungiyar za ta zama babban tafiya ta dalibai da zata taimaka wurin tabbatar da nasarar 'Renewed Hope'.

Ya ce:

"An kafa Tinubu/Shettima Students Vanguard ne don fadada manufofin Asiwaju Bola Tinubu da Sen Kashim Shettima, na zama shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa kamar yadda aka jero.
"Za a cimma hakan ne ta hanyar ilimantarwa, wayarwa da tattaro kan dukkan daliban masu zabe a jami'o'in Najeriya.
"Hakan zai tabbatar da kafa gwamnati mai kyau kuma yayin yin hakan za koyar da al'adar mulki mai kyau da sake wayar da kai a jami'o'in mu.
"Zai kuma fada musu dalilin da yasa Asiwaju Bola Tinubu da Sanata Kashim Shettima ne yan takara mafi cancanta a yanzu."

Asefon ya kara da cewa mambobin kungiyar a shirye suke su sauya zuciyar yan Najeriya kuma su zaburar da son kasa da aiki tukuru a zukatansu.

Kara karanta wannan

2023: Ahlus Sunnah, 'yan Tijjaniyah, 'yan Kadiriyah, CAN da 'yan kasuwa za su zabi Tinubu

Ya kara da cewa:

"Muna kira ga yan Najeriya su taho tare da mu a wannan tafiyar."

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

A wani rahoton, duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.

Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164