Ba Zamu Yarda Wani Kirista Ya Zabi Tinubu Ba Sai Shettima Yayi Murabus: Gamayyar Fastocin Arewa

Ba Zamu Yarda Wani Kirista Ya Zabi Tinubu Ba Sai Shettima Yayi Murabus: Gamayyar Fastocin Arewa

  • Gamayyar Malaman addinin Kirista a Arewacin Najeriya sun hadu a Abuja don zama kan lamarin APC
  • Fastocin sun yiwa jam'iyyar APC gargadin ta gaggauta tilastawa Kashim Shettima murabus sannan a mayeshi da wani Kirista
  • Jam'iyyar APC za ta shiga zaben shugaban kasan 2023 da Shugaba Musulmi, Mataimaki Musulmi

Kimanin Limaman addinin Kirista 500 daga Arewacin Najeriya sun hadu a Abuja don jaddada rashin amincewarsu da tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Gamayyar Malaman sun bayyana cewa idan ba'ayi abinda suke so ba, Bola Tinubu ya manta da kuri'unsu.

Kungiyoyin sun hadu ne ranar Talata domin duba sunayen Kiristocin da jam'iyyar APC ta sanya a kwamitin kamfenta, rahoton Sahara Reporters.

Sun ce idan ba'a tsige Kashim Shettima matsayin abokn tafiyar Tinubu ba, APC za tayi rashin goyon bayan miliyoyin mabiyansu a fadin tarayya.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin Da Yasa Duk Rintsi Ni da Mabiya Na Zamu Zabi Bola Tinubu, Babban Malami Ya Magantu

Kiristcon Arewa
Ba Zamu Yarda Wani Kirista Ya Zabi Tinubu Ba Sai Shettima Yayi Murabus: Gamayyar Fastocin Arewa Hoto: @saharareporters
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun bayyana haka a takardar da suka saki bayan taron a Abuja wanda Fasto Lucas Bako, Fasto Dauda Yakubu, Fasto Yiguda Augustine, Diconess Jessica Nuhu, Elder Williams Unogwu, Dr. Theodore Uji, Pst. Ambas Kelvin, Mr. Haruna Vincent da Bish Emeka, suka rattafa hannu.

A cewar jawabin:

"Shugabannin APC su tabbatar da cewa dan takaran mataimakin shugaban kasa yayi murabus da gaggawa. Kamar yadda aka bayyana a sabon dokar zabe, a sa shi ya aike wasika da kansa ga INEC cewa zai janye daga zabe."
"Idan yayi hakan zai jam'iyyar ta sanar da INEC, hakan zai sa a sauya dan takaran mataimakin shugaban cikin sauki."
"Idan APC ta samu kwararren Kirista ya jagorancin kamfen zaben 2023, lallai zasu iya samun wanda zai maye Kashim Shettima. APC ta nemi Kiristocin Arewa dake jam'iyyarta wadanda suka taimaka wajen samun nasararta."

Kara karanta wannan

2023: Wasu Jiga-Jigan Jam'iyyar PDP Sun Yi Watsi da Atiku, Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Arewa

"Idan sukayi watsi da koke-kokenmu game da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023, wannan zai kara rabuwar kai kuma haddasa jam'iyyar fadi a zaben."

Dan Takarar APC Tinubu Ya Gana da Malaman Addinin Kirista a Jihar Kano, Ya Yi Musu Jawabi

A wani labarin kuwa,Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya gana da wasu manyan malaman addinin kirista a jihar Kano ta Arewa maso Yammacin Najeriya.

A wani bidiyon da aka yada na Tinubu, an bayyana lokacin da yake yi musu jawabi game da hadin kai da kuma zaman lafiya da kamanceceniya tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya.

Tinubu ya bayyana cewa, hanya daya Musulmai da Kiristoci ke bi wajen neman gafara, kamar dai yadda yazo a Al-Qur'ani a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel