2023: Abinda da Yasa Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Zama Magajin Buhari a 2023, Nkire
- Jigon APC, Chief Sam Nkire, yace bisa la'akari da rashin zaman lafiya a PDP, Tinubu ba zai sha wahala ba a 2023
- Mista Nkire yace tarihi ya nuna cewa idan gwamnoni 5 suka yi bore a PDP ba ta kai labari, hakan ke shirin maimaita kansa
- Ya gargaɗi jam'iyya mai mulki ta gaggauta rarrashin wasu kusoshi da suka fusata don tabbatar da haɗin kan cikin gida
Abuja - Wani jigon jam'iyyar APC na ƙasa, Chief Sam Nkire, yace ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai lashe babban zaben 2023 da ke tafe cikin sauki.
Mista Nkire ya kafa hujjar abinda ya sa ya yi wannan hasahen da ganin alamun gwamnoni 5 na babbar jam'iyyar adawa PDP ka iya janye goyon bayansu ga jam'iyyar.
Nkire, wanda ya kasance tsohon shugaban tawagar yan majalisu na jam'iyyar APC reshen jihar Abiya, ya yi wannan hasashen ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Abuja.
A rahoton jaridar Vanguard, Jigon ya haƙaito cewa tarihi na shirin maimaita kansa inda yace, "Duk lokacin da PDP ta rasa goyon bayan gwamnoni biyar ba ta kai labari a zaɓen shugaban ƙasa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abinda ya faru da PDP a 2014 zai maimaita kansa - Nkire
Jigon jam'iyya mai mulkin ya ƙara da cewa a shekarar 2014, jam'iyyar PDP ta rasa gwamnoninta guda biyar kuma ta sha ƙasa a zaɓen 2015 sakamakon faruwar haka.
"Ga dukkan alamu babbar jam'iyyar hamayya PDP ta gaza rarrashin gwamnoni biyar, hakan alamu ne dake nuna APC ta gyara zama a gadon mulki ta hanyar sake samun nasara kan PDP a zaɓe mai zuwa."
Budu da ƙari, Mista Nkire ya gargaɗi jam'iyyarsa cewa ta tashi tsaye ta rarrashi dukkanin mambobin da suka fusata musamman kusoshi masu faɗa a ji.
A wani labarin kuma Na Kusa da Gwamnan Arewa, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC
Makonni uku bayan fara kamfen 2023, jam'iyyar APC ta kara samun gagarumin goyon baya a jihar Sakkwato.
Hadimin gwamna Aminu Tambuwal da mataimakin shugaban PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da magoya bayansu.
Asali: Legit.ng