Tsohon Gwamna Kuma Babban Jigon PDP Ya Tsame Hannunsa Daga Tawagar Kamfen Atiku 2023

Tsohon Gwamna Kuma Babban Jigon PDP Ya Tsame Hannunsa Daga Tawagar Kamfen Atiku 2023

  • Tsohon Gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko, yace ba gudu ba ja da baya a fafutukar da suke na ganin an yi adalci da dai-daito a PDP
  • Mimiko ya kuma musanta rahoton da ake yaɗawa cewa ya shiga jerin tawagar yakin neman zaɓen Atiku, ya raba jiha da Wike
  • Yace har yanzun shi da sauran yan tawagarsa ba su sauka daga matsayarsu ta ganin ɗan kudu ya karɓi mulki ba

Ondo - Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ranar Laraba ya nesanta kansa ta kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa na PDP wanda jam'iyyar ta fitar jiya Talata.

Tribune Online ta rahoto cewa Mimiko ya jaddada kudirinsa na ganin ɗan kudu ya karɓi mulkin ƙasar nan a 2023 domin dai-daito da adalci.

Mimiko, a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Johm Paul Akinduro, ya musanta raba gari da gwamna Nyesom Wike da sauran yan tawagarsa.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Na Shirin Janye Wa Wani Ɗan Takara? Sabbin Bayanai Sun Fito

Tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko.
Tsohon Gwamna Kuma Babban Jigon PDP Ya Tsame Hannunsa Daga Tawagar Kamfen Atiku 2023 Hoto: tribune
Asali: UGC

Tsohon gwamnan ya nuna cewa bai rabu da tsagin Wike ba da fafutukar da suke na ganin an yi wa kudancin Najeriya adalci a cikin jam'iyyar PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bani da hannu a jerin mambobin kamfe - Mimiko

Mista Mimiko ya ƙara da cewa ba wanda ya tuntuɓe shi ko ya nemi shawarinsa gabanin sakin jerin sunayen, inda a cewarsa ba shi da hannu a tawagar kamfen baki ɗaya.

Yace rahoton da ake yaɗawa cewa shi zai jagoranci tawagar karyace tsantsa kuma wani yunkuri ne na gurbata lamarin da ɓata masa suna.

Wani sashin sanarwan tace:

"Mutane na ta kiran Olusegun Mimiko ta ko ina tare da turo sakonni daga masoya, abokan siyasa da dumbin magoya baya a lungu da sakon Ondo suna bukatar karin haske kan labarin da ake yaɗa wa cewa ya raba gari da tsagin Wike."

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP Ya Yi Barazanar Yin Murabus Daga Kujerar Gwamna Kan Sharadi Guda

"Rahoton da kuma jerin tawagar duk ba gaskiya bane kuma wani yunkuri ne na zuzuta abu da ɓata sunan Mimiko. Wajibi mu jaddada cewa ba wanda ga nemi Mimiko da shirin sanya shi a kwamitin kamfen PDP na Ondo."
"Yana nan kan bakarsa da yan tawagarsa da masu ruwa da tsakin PDP kan yaƙin da suke na ganin tsarin jam'iyyar ya yi dai-dai rabe-raben Najeriya matukar dagaske ana son haɗa kan ƙasar nan."

Tsohon gwamnan ya kuma roki ɗaukacin al'umma su yi fatali da jerin sunayen Inda ya jaddada cewa bai sauka daga kudirinsa na ganin mulki ya koma kudu ba.

A wani labarin kuma Gangamin Taron Kamfen PDP a Edo Ya Sake Fito da Rikicin Jam'iyyar, Atiku Ya Shiga Matsala

Gangamin taron yakin neman zaɓen shugaban kasa na PDP da ya gudana a jihar Edo ya kara fito da rikicin jam'iyyar.

Wasu gwamnoni dake kan madafun iko 5 sun kaurace wa taron, wasu kuma sun halarta ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan PDP Ya Caccaki Yan Takarar Shugaban Ƙasa Biyu, Yace Ba Zasu Kai Labari Ba a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262