Anambra da Jihohi 7 da Peter Obi Zai Iya Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa
- Takarar Peter Obi a zaben sabon shugaban kasa mai zuwa tana cigaba da motsa siyasar Najeriya
- Peter Obi ya samu karbuwa musamman a Kudancin Najeriya da wasu jihohi a Arewacin kasar nan
- Ana hasashen Jam’iyyar Labour Party za ta gwagwiyi kuri’un da Atiku Abubakar ya samu a 2019
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta kawo jihohin da ake tunanin jam’iyyar Labour Party za tayi wa Atiku Abubakar illa a zaben 2023.
1. Anambra
Peter Obi zai iya samun gagarumar galaba a Anambra domin daga jihar ya fito, kuma ya yi gwamna sau biyu, yana da magoya-baya a yankin.
2. Abia
Jihar Abia tana cikin jihohin PDP da suka samu sabani da Atiku Abubakar. Idan ba ayi sulhu ba, Peter Obi zai amfana da wannan baraka.
3. Enugu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shi ma Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi yana tare da bangaren Nyesom Wike, zai yi wahala PDP ta maimaita nasarar 2019 a 2023 a Enugu.
4. Ribas
Gwamna Nyesom Wike ya sha alwashin yakar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa. Akwai yiwuwar hakan ya taimaki LP a zaben 2023.
5. Kuros Ribas
Jam’iyyar PDP ba ta da gwamna a Kuros Riba, kuma APC ba ta da karfi sosai. Akwai jiga-jigan siyasar jihar da za su taimakawa takarar Peter Obi.
6. Taraba
Duk da karfin PDP, babu mamaki wasu yankunan jihar Taraba su zabi Peter Obi a badi, musamman yadda jam’iyyar LP ta ba John Ikenya takarar gwamna.
7. Benuwai
Alamu na kara nuna cewa Gwamna Samuel Ortom da manyan jihar Benuwai ba za su goyi bayan PDP a zaben shugaban kasa ba, watakila su zabi LP.
8. Filato
Ba abin mamaki ba ne tsohon gwamnan Anambra ya ba PDP har da APC mamaki a Filato. Ba wannan ne karon farko da LP ta ci zabe a jihar ba.
Dalilin komawar Rabiu Kwankwaso NNPP
Kun ji labari Dr. Rabiu Kwankwaso ya nemi Mohammed Jamu ya samu mukami a PDP, amma wasu jiga-jigan jam’iyya suka hana a ba shi kujerar.
A dalilin wannan ne Jamu yace aka fusata Rabiu Musa Kwankwaso har ta kai ya koma jam’iyyar NNPP yana takarar shugabancin kasa a 2023.
Asali: Legit.ng