Jerin Fitattun Jiga-Jigan 'Yan PDP Da Suka Yi Watsi Da Atiku Suka Rungumi Obi

Jerin Fitattun Jiga-Jigan 'Yan PDP Da Suka Yi Watsi Da Atiku Suka Rungumi Obi

Kimanin awanni 72 kafin yin zaben fidda gwani na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a watan Mayu, Peter Obi, daya daga cikin manyan masu neman takarar, ya janye kuma ya fita daga babban jam'iyyar ta hamayya.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra wanda daga bisani ya shiga jam'iyyar Labour Party ya kuma samu tikitin takarar shugaban kasar jam'iyyar.

Obi da Atiku
Jerin Fitattun Jiga-Jigan 'Yan PDP Da Suka Yi Watsi Da Atiku Suka Rungumi Obi. Hoto: Mr. Peter Obi, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Tun bayan nasararsa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Obi yana ta samun karbuwa gabanin babban zaben 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu zabukan jin ra'ayoyin mutane da aka gudanar a intanet ma sunyi nuni da cewa shi zai ci zaben.

Duk da ya ke yanzu ba ya PDP, wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar sun yi watsi da Atiku Abubakar (dan takarar shugaban kasa na PDP) sun bayyana goyon bayansu ga Obi.

Kara karanta wannan

2023: Motocin Yakin Neman Zaben PDP Na Wata Jiha Sun Ta Da Kura, Babu Hoton Atiku Abubakar

1. Dr Sampson Orji

Dr Samspon Orji, jigo a jam'iyyar PDP kuma tsohon mai neman takarar gwamna, ya ce zai zabi Obi a maimakon dan takarar shugaban kasar jam'iyyarsa, Atiku Abubakar, a babban zaben 2023.

Ya ce ayyukan da Obi ya yi a baya da cancantarsa sun fifita shi kan sauran ya takarar shugaban kasar, har da Atiku.

Orji ya kuma ce ba zai fita daga PDP ba.

2. Babatunde Gbadamosi

Babatunda Gbadamosi, tsohon dan takarar gwamna (African Democratic Party/2019), fitaccen dan takarar PDP ne a Jihar Legas.

Gbadamosi, wanda tsohon dan takarar sanata na Legas ta Gabas a PDP, ya koma LP don ya goyi bayan Obi.

Ya ce takarar Obi ya farfado ya sa ya dena cire rai cewa Najeriya za ta gyaru.

3. Cif Adesunbo Onitiri

Cif Adesunbo Onitiri, wani jigon PDP a jihar Legas, ya koma jam'iyyar Labour Party.

Onitiri ya kara da cewa yana goyon bayan Obi ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

4. Ogbeide Ifaluyi-Isibor

Ogbeide Ifaluyi-Isibor shima wani jigo na jam'iyyar PDP wanda ya bayyana goyon bayansa ga Obi kan Atiku.

Ifaluyi-Isibor ya ce har yanzu shi dan jam'iyyar PDP ne amma yana goyon bayan Obi ya ci zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Jigon na PDP shine Direktan Hada Kan Mutane, na Kungiyar 'Nigeria Diaspora Youth Coalition For Peter Obi'.

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

Duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.

Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164