2023: Atiku Ya Maida Zazzafan Martani Ga Bola Tinubu Kan Kalaman Dubai
- Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 yace ba wanda zai yarda da Tinubu da APC
- Da yake martani kan kalaman Tinubu a Kano ta bakin kakakinsa Paul Ibe, yace mutane na tantama kan abubuwa da dama tattare da ɗan takarar na APC
- Yayin ganawa da shugabannin Tijjaniyya a Kano, Tinubu, yace ba zai zama shugaban ƙasan wani lokaci ba
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace bai kamata a ɗauki ɗan takarar shugaban dake ɓoye rashin lafiyarsa dagaske ba.
Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, shi ne ya faɗi haƙa yayin da yake martani kan kalaman da ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi a wurin taronsa da Malaman Ɗarikar Tijjaniyya a Kano.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Tinubu, yayin da yake kafa misali da Atiku Abubakar, yace idan ya ci zaɓe ba zai zama shugaban kasan wani lokaci ba, wanda zai raba lokutansa tsakaninn Dubai da Najeriya.
Atiku dake neman zama shugaban kasa a inuwar PDP ya shafe mafi yawan lokacinsa a Dubai bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2019.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wata sanarwa, Mista Ibe, wanda ya nuna cewa bai kamata a ɗauki kalaman Tinubu dagaske ba, yace:
"Shugabancin ƙasa kamar Najeriya, ƙasa lamba ɗaya mai yawan al'umma a nahiyar bakaken fata, ba na masu wasan barkwanci bane."
"Matakan da ake bi a zaɓi shugaban ƙasa ba gangami bane, don haka har sai lokacin da APC ta iya haɗa gida ɗaya bai dace a ɗauke su dagaske ba saboda ba su da tsari."
"Ba wanda zai yarda da ɗan takarar shugaban ƙasa na waccan jam'iyyar (APC). Ba wanda zai ɗauki ɗan takarar da jam'iyyarsa wanda rashin lafiyarsa, karatunsa da shekaru duk kewaye suke da ɓoyayyen sirri."
FFK Ya Faɗi abinda ya sa suka koma APC
A wani labarin kuma Daraktan Midiya na kamfen Tinubu ya bayyana dalilin da yasa shi da wasu gwamnonin PDP suka koma APC
Daraktan midiya na tawagar kamfen Tinubu, Femi Fani Kayode, yace ya zaɓi komawa APC ne saboda abinda yake tsoro ya kauce a jam'iyyar.
Tsohon ministan yace sheɗanun da suka dabaibaiye APC sun yi ƙaura zuwa PDP, shiyasa shi da wasu gwamnoni suka fita.
Asali: Legit.ng