Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa

Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa

  • Mambobin jam'iyyar APC sun yi bikin wanke filin gangamin taron PDP a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina
  • Babbar jam'iyyar adawar kasar dai ta yi taron tarban sabbin mambobi 13,000 da suka sauya sheka daga APC da NNPP a yankin
  • Shugabannin APC a karamar hukumar sun kawo tankar ruwa sannan suka dukufa wanke wajen taron da tsintsiya

Katsina - An sha yar dirama jim kadan bayan babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta tarbi kimanin mutum 13,000 da suka sauya sheka zuwa cikinta a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

PDP dai ta yi sabbin mambobin ne wadanda suka fice daga jam’iyyun All Progressives Congress (APC) mai mulki da New Nigeria People’s Party, NNPP ta su Kwankwaso.

Yan APC
Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa Hoto: AIT
Asali: UGC

AIT ta rahoto cewa diramar ta fara ne lokacin da mambobin jam’iyyar APC a yankin karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar, Bashir Sabi’u Maitan, suka yiwa filin taron na PDP tsinke.

Kara karanta wannan

Na Kusa da Gwamnan Arewa, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Shugaban APC a karamar hukumar, Surajo Ado da sakataren jam’iyyar, Muhammed Lawal sun jagoranci kai motar tanka guda cike da ruwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan sun kai motar tankar, sai aka yi amfani da shi wajen wanke wajen taron karbar masu sauya shekar.

Ga karin hotuna a kasa:

Yan APC
Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa Hoto: AIT
Asali: UGC

Yan APC
Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa Hoto: AIT
Asali: UGC

Na Yi Kama Da Mara Lafiya? Takarar Shugaban Kasa Nake Nema Ba Gasar Yan Dambe Ba, In ji Tinubu

A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi watsi da rade-radin cewa bashi da cikakkiyar lafiya.

Yayin da yake jawabi ga taron jama’a a ranar Asabar, 22 ga watan Oktoba a jihar Kano, Tinubu ya ce shi takarar shugabancin kasa yake nema ban a yan dambe ba.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Abba Ganduje Da Laifin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati, An Kai Kararsa Wajen EFCC

Tsohon gwamnan na jihar Lagas cikin raha ya tambayi taron jama’ar da ke wajen kan ko ya yi kama da mara lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng