Da Duminsa: Buhari Ya Sha Alwashin Yi wa Tinubu Gagarumin Kamfen
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a yayin gangamin kamfen din zaben 2023
- Buhari ya bayyana cewa, cike da farin ciki ya karba shugabancin tawagar kwamitin kamfen din Bola Ahmed Tinubu na APC
- Ya kara da sanar da cewa, muhimmancin cin wannan zaben ga jam’iyyar APC har ya fi na zaben 2015 wanda ya kai shi kujerar da yake
FCT, Abuja - Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kasancewa a sahun gaba wurin gangamin yakin neman zaben ‘dan takarar shugabancin kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu.
Yace akwai matukar amfani idan jam’iyyar ta cigaba da rike shugabancin kasa domin cigaba kan nasarorin da suka samu a shekaru bakwai da suka gabata, jaridar The Nation ta rahoto.
Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin kaddamar da tawagar kamfen din shugabancin kasa na APC tare da kaddamar da shirin Tinubu a Abuja.
Shugaban kasan wanda yayi jawabi a wurin, yayi kira ga mambobin jam’iyyar APC da suyi aiki tukuru wurin ganin nasarar kamfen din.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yace:
“Zai kasance babban ibtila’i a zuba ido a ga lalacewar cigaban kasar da muka kawo. Bari in sanar da cewa cike da farin ciki na karba matsayin shugaban tawagar kamfen din da na kaddamar a yau.
“‘Dan takararmu, Asiwaju Bola Tinubu sananne ne kan abinda zai iya yi. A tsaye yake gyam kan tarihin da ga bari matsayin ‘dan damokaradiyya, masanin dokoki kuma shugaba mai hangen nesa.
“A don haka nake son tabbatar da dukkan mambobin jam’iyyar mu da magoya bayan gwamnati mu cewa zan kasance a sahun gaba wurin wannan kamfen.
“Wannan zaben yafi muhimmanci fiye da zaben 2015 da ya kawo mu kan mulki.”
Kwamitin Takara: Fasto ya Kunyata APC, Yace Ba Zai Yi Wa Tinubu Kamfe a 2023 ba
A wani labari na daban, Rabaren Gideon Para-Mallam ya ki amincewa ya yi wa jam’iyyar APC aiki bayan an sa shi a ‘yan kwamitin neman zaben shugaban Najeriya.
Rabaren Gideon Para-Mallam ya yi watsi da wannan aiki ne lura da matsayin da kungiyar CAN ta dauko, Vanguard ta fitar da wannan rahoto a dazu.
Malamin addinin yace babu abin da ya hada shi da siyasar jam’iyya, amma yana tare da kungiyar kiristocin Najeriya da ke adawa da tikitin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng