Sunayen da Aka Kara da Wadanda Aka yi Watsi da su a Kwamitin Neman Takarar Tinubu

Sunayen da Aka Kara da Wadanda Aka yi Watsi da su a Kwamitin Neman Takarar Tinubu

  • Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fadada kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa
  • Mai girma Muhammadu Buhari wanda shi ne shugaban kwamitin, zai kaddamar da PCC a fadar Aso Villa
  • Har yanzu ba a sa sunan tsohon SGF, Babachir Lawal da tsohon shugaban majalisa, Yakubu Dogara ba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne shugaban majalisar kamfe, yayin da aka maida Abdullahi Adamu ya zama mataimakin shugaban majalisa.

Asiwaju Bola Tinubu ya koma mataimakin shugaban majalisar kamfe na II a sabon jerin, shi ma Kashim Shettima zai rike mataimakin shugaban kwamitin.

Premium Times tace tsohon gwamnan Borno, kuma ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Shettima zai jagoranci kwamitin nemo kudin kamfe.

Har yanzu Hon. James Faleke ne sakataren majalisar yakin neman zaben. ‘Dan majalisar na Legas yana cikin na-hannun daman Bola Tinubu mai takara a 2023.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jam'iyyar APC Ta Fitar da Sunayen Tawagar Kamfen 2023 Na Karshe, An Samu Sauyi

An sa duka 'Yan NWC

Jaridar tace cikakken jerin da ya fito yana dauke da duk ‘yan kwamitoci da jagororin kwamitin PCC da zai taya Bola Tinubu neman zama shugaban kasa a badi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A halin yanzu kwamitin na PCC yana dauke da duka ‘yan APC da ke majalisar tarayya, duk ‘yan majalisar zartarwa na kasa na FEC da ‘yan majalisar NWC.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a taron Ministoci Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Rahoton ya kara da cewa an hada da sunayen dukkanin tsofaffin gwamnoni da tsofaffin mataimakan gwamnoni da suke tare da jam’iyyar APC mai mulki.

Har tsofaffin shugabannin jam’iyyar APC na kasa da wadanda suka taba zama a majalisar koli ta NEC sun shiga jerin kwamitin yakin neman takaran na 2023.

Ragowar sun hada da shugabannin majalisar dokoki na jihohi da mataimakansu masu-ci da wadanda suka bar ofis da kuma shugabannin jam’iyya na jihohi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Biyu a Arewa

Duk wani wanda ya yi takarar majalisar tarayya ko ta jiha a APC ya shiga sabon jerin. Wani rahoton yace Musiliu Akinsanya watau MC Olumo ya samu shiga.

Wadanda babu sunansu har yanzu

  1. Yemi Osinbajo
  2. Babachir Lawal
  3. Yakubu Dogara
  4. Osita Okechukwu
  5. Adebayo Shittu

Wadanda aka sa sunansu yanzu

  1. Shina Peters
  2. Kashim Shettima
  3. Dr Mahmood Ahmed
  4. Imman Ibrahim
  5. Janar Cecil Esekhaigbe
  6. MC Olumo

'Yan kwamitin PCC sun karu

Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da sabon jerin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a 2023 da sa hannun Sakataren APC, Iyiola Omisore.

Kun ji labari Sanata Iyiola Omisore ya fitar da kwamitin a ranar 19 ga watan Oktoba 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng