Yadda Tinubu Zai Lashe Zabe a Arewa, Ya Dare Kujerar Shugaban Kasa a 2023, Dan Kashenin Buhari
- Alhaji AbdulMajid Danbilki Kwamanda, ya nuna karfin gwiwa cewa Bola Ahmed Tinubu zai lashe kuri'un al'ummar arewa a zaben shugaban kasa na 2023
- Danbilki wanda ya kasance dan kashenin shugaban kasa Buhari ya ce Tinubu na da abubuwan bukata domin sauya akalar tattalin arzikin kasar nan
- Jigon na APC ya kuma jadadda cewa tsohon gwamnan na jihar Lagas na kara samun farin jini da karbuwa a tsakanin yan Najeriya
Kano - Jigon jam’iyyar APC kuma babban dan kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji AbdulMajid Danbilki Kwamanda, ya yi hasashen abun da zai faru a babban zaben kasar mai zuwa.
Danbilki Kwamanda ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, Bola Ahmed Tinubu, zai yi ci mai kyau a zaben 2023 duba ga yadda yake kara samun karbuwa da farin jini a yanzu haka, Nigerian Tribune ta rahoto.
Kwamanda wanda shine jagoran kungiyar yada muradin dan takarar a arewa, ya yi hasashen ne a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba, a Kano yayin da yake zantawa da manema labarai.
Ya ce nasarar Tinubu a zaben shugabar kasar kamar anyi an gama ne saboda APC da arewa na so shugabancin kasar ya koma yankin kudu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
“Kun dai gani har yanzu hannun Bola Tinubu na aiki a Lagas inda shi kadai ya juya akalar tattalin arzikinta inda ya mayar da ita cibiyar tattalin arzikin nahiyar Afrika ta Yamma.
“Jiya jiyan nan Lagas ke fadawa kowa cewa sun tara sama da biliyan N700 a matsayin kudaden shiga a 2021. Ta yaya suka yi wannan abun idan ba don Bola Tinubu ba? Don haka, yan Najeriya na burin ganinsa yayi nasara a zaben shekara mai zuwa.”
Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023
Alhaji Kwamanda wanda ya kasance dan kashenin Buhari tun a 2000 yace Najeriyar yau ba za ta taba komawa zamanin PDP/Atiku ba.
Ya kuma bayyana cewa ya rigada ya mamaye yankin arewacin Najeriya kuma ya yarda cewa yankin na bayan Tinubu dari bisa dari.
Kan tattalin arziki, ya tunatar da yan Najeriya cewa ba sai an fada ma mutum cewa Bola Tinubu na da abun bukata don saita Najeriya ba a zangonsa na farko da na biyu.
Ya kuma ce tsohon gwamnan zai janyo hankalin masu zuba jari na kasashen waje yayin da yake bunkasa tattalin arziki kamar yadda ya yiwa jihar Lagas.
Tinubu Zai Kare Muradun Arewacin Najeriya, Sanata Abu Ibrahim
A gefe guda, tsohon Sanata da ya wakilci Katsina Ta Kudu a majalisar dattawa, Abu Ibrahim, ya bayyana cewa dan takaran kujeran shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, zai kare muradun Arewa.
Ibrahim ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda ya ziyarci ofishin kamfen Dikko Radda dan takarar gwamnan jihar na APC.
Sanatan yace lokaci ya yi da ya kamata Arewa ta mayarwa Tinubu alherin da ya yiwa yan yankin ta hanyar kada masa kuri'a, rahoton NAN.
Asali: Legit.ng