Zaben 2023: Kada Ku Zabi Duk Wanda Yace Abubuwa Zasu Yi Sauki, Sanusi Ga Yan Najeriya

Zaben 2023: Kada Ku Zabi Duk Wanda Yace Abubuwa Zasu Yi Sauki, Sanusi Ga Yan Najeriya

  • Gabannin zaben 2023, Muhammadu Sanusi II ya ce kada yan Najeriya su zabi duk dan takarar da yace abubuwa zasu yi sauki idan aka zabe shi
  • Tsohon sarkin Kanon ya ce imma dai mai shi yana masu karya ne ko kuma bai san aikin da yake son samu ba
  • Khalifan na darikar Tijanniya ya ce yana tausayawa wanda zai karbi shugabancin Najeriya daga hannun Buhari

Kaduna Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci yan Najeriya da kada su zabi duk dan takarar shugaban kasar da yayi ikirarin cewa abubuwa zasu yi sauki da zarar an zabe shi a 2023.

Sanusi wanda ya kasance shugaban darikar Tijanniya na kasa ya bayyana hakan a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a wajen rufe taron tattalin arziki da zuba hannun jari na Kaduna, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Zan Dora Daga Inda Shugaba Buhari Ya Tsaya, Bola Tinubu

El-Rufai da Sanusi II
Zaben 2023: Kada Ku Zabi Duk Wanda Yace Abubuwa Zasu Yi Sauki, Sanusi Ga Yan Najeriya Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Ya ce:

“Dan Allah bari na nemi wani abu daga yan siyasarmu. Dole ku shirya zukatan yan Najeriya game da daukar matakai masu wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duk wanda ya fada maku cewa abubuwa zasu yi sauki, dan Allah kada ku zabe shi. Imma dai yana maku karya ko kuma bai san wani irin aiki zai samu bane.
“Da wannan tarin basussuka, da wannan tarin rugujewa a kudaden shiga, da wannan talauci, ba z aka iya daukar matakan daidai ba. Ya zama dole a gyara haraji kan ma’aikatar lantarki. Ya zama dole a gyara haraji a ma’aikatar mai.
“Amma kafin a gyara wannan, dole mu magance damammaki na neman rancen kudi. Ya zama dole a dinke barakar da ke lambobin, lambobin karyan.”

Channels TV ta kuma rahoto cewa Sanusi ya ce yana tausayin wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari duba da yadda tattalin arziki ta tabarbare

Kara karanta wannan

Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu

.Sarkin Kanon na 14 ya ce tattalin arzikin kasar ya dogara ne ga man fetur da iskar gas kuma cire tallafi yana kara gurgunta tattalin arzikin.

2023: Zan Dora Daga Inda Shugaba Buhari Ya Tsaya, Bola Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya bayyana cewa zai dora daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya idan har aka zabe shi a 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron tattalin arziki da zuba hannun jari na jihar Kaduna a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, Premium Times ta rahoto.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ba jama’ar da suka taru tabbacin cewa shine zai lashe zaben shugaban kasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng