2023: Zan Dora Daga Inda Shugaba Buhari Ya Tsaya, Bola Tinubu

2023: Zan Dora Daga Inda Shugaba Buhari Ya Tsaya, Bola Tinubu

  • Gabannin zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ya sha alwashin dorawa daga inda Buhari ya tsaya
  • Tinubu wanda ya nuna karfin gwiwar cewa shine zai lashe zabe, ya ce zai bayar da fifiko wajen inganta manufar saukaka kasuwanci
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya kuma jadadda cewa zai zuba jari a bangaren more rayuwa

Kaduna - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya bayyana cewa zai dora daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya idan har aka zabe shi a 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron tattalin arziki da zuba hannun jari na jihar Kaduna a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ba jama’ar da suka taru tabbacin cewa shine zai lashe zaben shugaban kasa mai zuwa.

Bola Tinubu
2023: Zan Dora Daga Inda Shugaba Buhari Ya Tsaya, Bola Tinubu Hoto: The Governor Of Kaduna
Asali: Facebook

Ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen inganta manufar saukaka kasuwanci na gwamnati mai ci da kuma zuba jari a bangaren more rayuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya bayyana cewa zuba jarin kamfanoni masu zaman kansu shine tushen gina tattalin arziki mai tasiri. Ya bayyana cewa za a samar da abubuwan bukata ga bangaren kasuwanci.

Ya ce:

“Gwamnatin shugaba Buhari ta samar da wasu matakai da nufin inganta kamfanoni masu zaman kansu, da suka hada da sokewa da kuma sake amfani da tsarin CAMA 2020, aiwatar da dokar kudi ta 2021, da kuma aiwatar da tsare-tsare sama da 100 don ingata yadda za a tafiyar da kasuwanci a kwana daya.
“Na tsaya a gabanku-ba zaku girbe masara a ranar da aka shuga irin ba. Muna kan hanya madaidaiciya, kuma zamu gina kasa.”

Kara karanta wannan

Yadda Zan Tsaya Na Yaki Yan Bindiga Idan Na Zama Shugaban Kasa a 2023, Tinubu

Ya kuma yi alkawarin gyara bangaren shari’a da zai tabbatar da doka a kasar nan yana mai cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da ganin cewa an yi amfani da fasaha wajen gudanar da gwamnati don tabbatar da inganci.

Zan Tsaya Tsayin Daka Na Yaki Yan Bindiga Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu

A gefe guda, mun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin yakar yan fashin daji da suka addabi mutane idan ya zama shugaban ƙasa a 2023.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan Legas ɗin ya yi wannan furucin ne a wurin taron tattalin arziki da zuba hannun jari karo na Bakwai a Kaduna.

Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya karkashin jam'iyya mai mulki ya kara da cewa yana da tabbacin zai iya jagorantar kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel