Lamari Ya Dagule Bayan Atiku Yace Arewa Bata Bukatar Bayerabe Ko Ibo Ya Mulki Najeriya a 2023
- Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, lamura na kara dagulewa a bangaren dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar
- Atiku ya bayyana cewa yan arewa basa bukatar dan takara Bayarabe ko Ibo ya mulke su a 2023
- Wannan furuci na tsohon mataimakin shugaban kasar ya tunzura mutane da dama, inda suka zarge shi da kada gangar kabilanci
Furucin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayi na cewa yan arewa basa bukatar dan Ibo ko Bayarabe ya shugabancesu ya bar baya da kura, PM News ta rahoto.
A wani bidiyo da ya yadu, an jiyo Atiku yana cewa shi ya fahimci gaba daya yankunan kasar kuma abun da yan arewa suka fi bukata a yanzu shine wani daga arewa ya shugabance su.
Ya ce:
“Yan arewa basa bukatar dan takara Bayarebe ko dan takara Ibo ya shugabance su.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan Najeriya da suka je shafukan soshiyal midiya don yin martani kan furucin nasa, sun zargi Atiku da kada gangar kabilanci don ganin ya samu kuri’un arewa, jaridar PM News ta rahoto.
Ga martanin jama’a a kasa:
Festus Keyamo, kakakin kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC yace ya kamata Atiku ya fita daga tseren shugabancin kasar a yau saboda yana son amfani da kabilanci wajen kamfen.
Raheem Yisa Akorede ya ce:
“Eh yana amfani da kabilanci a yanzu saboda ya san bashi da hanyar lashe wannan zaben.”
Omo Ologo ya kara da cewa:
"Mai hada kai ya shiga hanyar tada hankali.”
Nkem ta rubuta:
“Atiku Abubakar wanda ya fake a karkashin kasancewa “mai hada kai” yana fada ma yan arewa cewa basa bukatar dan takara Bayarabe ko Ibo. Wannan na tabbatar da cewa tikitin Obi Datti da masu goyon bayan tafiyar ‘Obidient’ ke tallatawa shine kadai ke son hada kan al’umma.”
Yaikuub ya ce:
"Atiku Abubakar ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.”
Atiku: Yan Arewa Na Bukatar Dan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa Ba Bayarabe Ko Inyamuri Ba
A wani labarin, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yan arewa na bukatar wani shugaban kasa da ya fito daga yankin arewacin kasar.
Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a wani taron yan arewa da aka gudanar a jihar Kaduna, The Cable ta rahoto.
Yayin da yake jawabi ga taron al’ummar Hausa Fulani da dama, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa basa bukatar dan Igbo ko bayarabe a matsayin shugaban kasa sai dai wani daga arewa.
Asali: Legit.ng