2023: Manyan Alkawurra Uku da Atiku Ya Daukar Wa Jagororin Arewa a Kaduna
- Atiku Abubakar ya yi alkawarin magance matsalar tsaro da ya addabi yankin arewa idan ya ɗare shugaban kasa a 2023
- Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a inuwar PDP yace ya shirya tsaf wajen tsamo tattalin arzikin kasar nan daga durkushe wa
- Shugabannin yankin arewa sun gabatar wa Atiku muhimman kalubalen da suke so a magance musu
Kaduna - A ranar Asabar, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya gana da shugabannin kungiyar Arewa Consultative Forum da wasu kungiyoyin arewa a Kaduna.
Channels tv ta ruwaito cewa yayin ganawarsu, Atiku ya gabatarwa jagororin arewa ajenda da kudirorinsa idan ya zama shugaban kasa a zaɓen 2023.
Da yake jawabi ga taron shugabannin arewan, tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ɗauki alkawurra uku masu matuƙar muhimmanci idan Allah ya ba shi nasara a zaɓe.
Atiku ya tabbatar musu da cewa zai magance matsalar tsaron da ta addabi yankin arewa karkashin mulkin APC, haɓaka tattalin arzikin da ya kama hanyar durkushe wa da kuma abu mafi muhimmanci haɗa kan kowane yanki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane bukatu shugabannin arewa suka mika wa Atiku?
Ɗaya daga cikin jagororin arewa, Munir Jafaru, ya gabatar wa mai neman ɗare wa kujerar shugaban ƙasa a inuwar PDP wasu daga cikin kalubalen da suka wa yankin katutu.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa daga cikin kalubalen da suka baje wa Atiku a Teburi sun haɗa da, rashin tsaro, talauci da kuma jahilci da ya yawaita duk a arewa.
Jafaru ya ƙara da cewa arewa zata goyi bayan duk ɗam takarar da ke da mafi kyaun kudirin shawo ƙan matsalolin da yankin ke fama da su.
A wani labarin kuma Kungiyar Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a Kano da Wasu Jihohi 18 Ta Juya Masa Baya
Wata ƙungiyar magoya bayan Atiku Abubakar a Kano ta sanar da janye wa daga goyon bayan ɗan takarar na PDP.
Shugaban kungiyar yace mutane sama da Miliyan biyu daga jihohin arewa da Abuja sun ce ba zasu ci gaba da mara wa Atiku baya ba.
Asali: Legit.ng