Kungiyar Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a Kano da Wasu Jihohi 18 Ta Juya Masa Baya

Kungiyar Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a Kano da Wasu Jihohi 18 Ta Juya Masa Baya

  • Wata ƙungiyar magoya bayan Atiku Abubakar a Kano ta sanar da janye wa daga goyon bayan ɗan takarar na PDP
  • Shugaban kungiyar yace mutane sama da Miliyan biyu daga jihohin arewa da Abuja sun ce ba zasu ci gaba da mara wa Atiku baya ba
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jam'iyyar PDP ta buɗe babin yakin neman zaben Atiku/Okowa 2023

Kano - Wata Ƙungiyar dake kokarin tallata mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da ake kira da Arewa Reporters ta raba gari da shi a jihar Kano.

Jaridar Aminiya ta ruwaito shugaban ƙungiyar, Abdullahi A. Gana, na cewa mambobi miliyan biyu ko fiye da haka daga jihohin arewa 19 da Abuja ne suka jingine goyon bayansu ga Atiku.

Kara karanta wannan

2023: Ana Shirin Bude Kamfe Yau, Atiku Ya Dauki Matakin Karshe Kan Rikicinsa da Gwamna Wike

Atiku Abubakar.
Kunguyar Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a Kano da Wasu Jihohi 18 Ta Juya Masa Baya Hoto: aminiya
Asali: Depositphotos

Ya ƙara da cewa mambobin ƙungiyar da shugabannin sun ɗauki matakin juya wa Atiku baya ne saboda zargin rashin adalci da kuma watsi da su baki ɗaya.

Bugu da ƙari, shugaban Arewa Reporters, ya yi zargin cewa babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP tana nuna musu wariya a harkokin da suka shafi Atiku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wane mataki ƙungiyar ta ɗauka?

"Daga yau, wannan ƙungiyar ta mu ta jingine goyon bayanta ga Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP. Ba zai yuwu mu cigaba da yin siyasa tamkar bayi ba, ko me ka yunkuro zaka yi sai a kafa sharaɗin sai an ci zaɓe za'a saka maka."
"Mun je wurin ɗan takara (Atiku) muka zuba mai a Motocinmu muka kama Hotel, sannan muka yi wa mambobin da suka halarta ihisani, amma aka ce sai an ci mulki za'a saka mana, to idan aka sha ƙasa fa?"

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Kwankwaso? An Bayyana Dan Takarar Da Ya Shirya Ceto Najeriya Idan Ya Gaji Buhari a 2023

- Abdullahi Gana.

Ina zasu koma yanzu a siyasance?

Mista Gana ya bayyana cewa za su cigaba da nazari da neman shawari domin yanke inda ƙungiyar zata dosa nan gaba.

A wani labarin kuma Kun ji cewa Kotun Koli Ta Zabi Ranar Raba Gardama Kan Wanda Zai Gaji Abokin Takarar Atiku a 2023

Kotun Koli zata raba gardama kan tikitin jam'iyyar PDP na takarar gwamnan jihar Delta a zaɓen 2023 da ke tafe.

Tawagar Alkalai biyar dake sauraron ƙarar sun zaɓi ranar 21 ga watan Oktoba, 2022 domin kawo karahen shari'ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel