Zan Tsaya Tsayin Daka Na Yaki Yan Bindiga Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu
- Mai neman zama shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, yace ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen kawar da yan bindiga idan ya ci zaɓen 2023
- Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin yace yana da kwarewa da duk abinda ake bukata na jagorantar Najeriya
- Tinubu ya bayyana haka ne a wurin taron tattalin arziki da zuba hannun jari karo na Bakwai da aka shirya a Kaduna
Kaduna - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin yakar yan fashin daji da suka addabi mutane idan ya zama shugaban ƙasa a 2023.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan Legas ɗin ya yi wannan furucin ne a wurin taron tattalin arziki da zuba hannun jari karo na Bakwai a Kaduna.
Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya karkashin jam'iyya mai mulki ya kara da cewa yana da tabbacin zai iya jagorantar kasar nan.
Haka zalika ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa zai magance baki ɗaya matsalolin da suka yi wa ƙasar nan katutu matuƙar suka dangwala masa kuri'u ya zama shugaban ƙasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar Punch ta rahoto Tinubu yace:
"Idan kuka bar ni a kan dandamalin nan zan ci gaba da kamfe ne, zan roki El-Rufai kar ya bar Najeriya a 2023 domin muna bukatar kwarewarsa a dai-dai wannan lokacin."
"Ina da kwarin guiwar faɗa muku cewa zan iya jagorancin ƙasar nan a 2023 idan kuka goya mun baya. Ina da kwarewar shawo kan baki ɗaya matsalolin nan kuma na dawo da ƙasar nan kan turba mai kyau da ci gaba."
Ta Fasu: Kalaman da Tinubu Ya Nemi Tawagar Matan APC Su Faɗa Wa 'Yan Najeriya Masu Neman Canji a 2023
"Ba inci ɗaya na kasar nan da zamu bari ana aikata ta'addancin yan fashin daji, zamu yaƙe su ba tare da gazawa ba. A karkashin mulki na zamu yi amfani da fashaha wajen yakar manyan laifuka kuma zamu tsare rayukanku."
Atiku ya gamu da cikas a Arewa
A wani labarin kuma Kungiyar Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a Kano da Wasu Jihohi 18 Ta Juya Masa Baya
Wata ƙungiyar magoya bayan Atiku Abubakar a Kano ta sanar da janye wa daga goyon bayan ɗan takarar na PDP.
Shugaban kungiyar yace mutane sama da Miliyan biyu daga jihohin arewa da Abuja sun ce ba zasu ci gaba da mara wa Atiku baya ba.
Asali: Legit.ng