Tashin Hankali Ga APC, Jiga-Jiganta a Rivers Sun Sha Alwashin Yiwa Atiku Aiki

Tashin Hankali Ga APC, Jiga-Jiganta a Rivers Sun Sha Alwashin Yiwa Atiku Aiki

  • Wasu mambobin jam'iyyar PDP a jihar Ribas sun sauya sheka yayin da ake tsaka da shirin babban zaben 2023
  • Hakazalika, sun bayyana komawa jam'iyyar PDP tare da cewa za su marawa Atiku baya a zaben 2023 mai zuwa
  • Ana yawan samun guguwar sauya sheka a Najeriya yayin da kasar ke shirin zabe a shekara mai zuwa

Jihar Ribas - Iskar guguwar sauya sheka na kara kadawa a jam'iyyar APC a 'yan kwanakin nan, jiga-jigan jam'iyyar sun sauya sheka a karamar hukumar Ogu-Bolo zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

A yau Alhamis 13 ga watan Oktoba ne labari ya iso mu cewa, wasu jiga-jigan APC a jihar Ribas sun sauka sheka tare da bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, Rivers Mirror ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Daruruwan 'Ya'Yan APC a Mazabar Gwamnan Arewa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Jiga-jigan APC sun koma PDP a jihar Ribas
Tashin Hankali Ga APC, Jiga-Jiganta a Rivers Sun Sha Alwashin Yiwa Atiku Aiki | Hoto: @Rivers Mirror
Asali: Facebook

Da yake zantawa da wadanda suka sauya shekan, shugaban karamar hukumar Ogu/Bola a jihar Ribas, Hon. Vincent Nemieboka ya bayyana musu cewa, PDP za ta basu duk wani gata da suke bukata.

Za mu gabatar daku ga sauran mambobin PDP, inji Hon. Vincent

Ya kuma bayyana cewa, nan ba da dadewa jam'iyyar PDP za ta gabatar da wadannan sabbin mambobi da suka bar APC da ma sauran jam'iyyu ga sauran mambobin PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake gabatar dasu ga shugaban karamar hukumar, Hon Tamunosiki Tiene, wanda shine tsohon shugaban APC a karamar da ya sauya sheka zuwa PDP a baya, ya ce wadanda suka sauya shekan sun fito ne daga gundumomi 11 na yankin Wakama.

Kofa a bude take ga duk wadanda ke son shiga PDP

Hon Tamunosiki Tiene ya shaida cewa, wadanda suka sauya shekan sun same shi ne tare da bayyana sha'awar shiga tafiyar PDP, shi kuwa yace musu lemar PDP da sauran inuwa kawai su shigo su dana.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu a jihar Arewa, dubban mambobin APC sun koma PDP, sun zabi Atiku

Ya kuma ce sun shaida masa cewa sun gaji da rikon tsintsiya babu shara tare da cewa suna sha'awar shan inuwar PDP.

Dalilin da yasa suka sauya sheka

Da yake magana a madadin wadanda suka sauya shekan, Mr. Fyneface Wakama ya ce suna sha'awar abubuwan dake faruwa a jam'iyyar PDP, wannan yasa suka yanke shawarin shiga cikinta.

Ya kuma bayyana cewa, yanzu haka suna wakiltar wasu gungun jama'a ne dake kauna da sha'awar neman mafaka a PDP.

Hakazalika, ya ce za su yi aiki tukuru don ganin jam'iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa a kujeru daban-daban daga sama har kasa sak.

Daga nan ne aka karbe su hannu bibbiyu tare da marabtar cigaban da suka zo dashi.

Ta kwabewa APC da Tinubu, mambobin APC 2000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

A wani labarin, a ranar Laraba 12 ga watan Oktoba ne wasu mambobin APC akalla 2000 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ta dawa a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Bindiga Sun Bude Wuta a Wurin Taron da Aka Shirya Domin Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa

A cewar mambobin da suka saki APC, ba za su ci gaba da zama a jam'iyyar da Buhari ya yi alkawari amma ya gaza cikawa ba, haka nan gwamnansu Mai Mala Buni.

Sabbin mambobin na jam'iyyar PDP sun kuma bayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zabe mai zuwa, Rivers Mirror ta tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.