'Yan Bindiga Sun Kara Kai Hari Wurin Taron Mambobin Jam'iyyar LP A Jihar Enugu

'Yan Bindiga Sun Kara Kai Hari Wurin Taron Mambobin Jam'iyyar LP A Jihar Enugu

  • Tsagerun yan bindiga sun sake tarwatsa taron mambobin jam'iyyar LP wacce Peter Obi ke takarar shugaban kasa a Enugu
  • Rahotannin da aka tattara sun nuna cewa maharan sun buɗe wuta a iska bayan kutsa wa wurin a Umuida, ƙaramar hukumar Igbo-Eze ta arewa
  • Wata majiya tace maharan sun kona mota, Babura da kuma Keke-Napep da suka taras a wurin

Enugu - A ranar Lahadi da ta gabata, wasu 'yan bindiga suka tarwatsa taron jam'iyyar Labour Party (LP) ta Peter Obi a Umuida, ƙaramar hukumar Igbo-Eze ta arewa jihar Enugu.

Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigan sun isa wurin a Babura biyu, suka buɗe wuta a saman iska, suka tarwatsa mambobin jam'iyyar kana suka babbake motoci, Napep da Baburan wurin.

Kara karanta wannan

Mata da Yara 30 Sun Yi Shahada, Sun Nutse a Ruwa Za Su Tserewa ‘Yan Bindiga

Taswirar jihar Enugu.
'Yan Bindiga Sun Kara Kai Hari Wurin Taron Mambobin Jam'iyyar LP A Jihar Enugu Hoto: vanguard
Asali: UGC

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta, tace harin ya auku ne a wuraren taruka biyu, Umu Aji da Nkwo Iyida inda magoya bayan LP ke ganawa da juna.

Majiyar ta kuma nuna damuwarta bisa yawaitar kai wa mambobin jam'iyyar LP hari yayin da suke gudanar da taro, inda ta ƙara da cewa mai yuwuwa lamarin na da alaƙa da siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce:

"Muna tsaka da taro lokacin da wasu mutum huɗu a kan Babura biyu suka iso wurin, suka fara harbe-harben bindiga a saman iska, nan take kowa ya yi takansa domin tsira."
"Shugaban gunduma da wasu mambobi suka gudu suka bar Makullan motocinsu a kan Teburi, mun gano maharan sun ƙona Babura da Keke-Napep. Sannan kuam sun tafi da wata Mota Camry."
"Bayan wani ɗan lokaci, sakamakon wata matsala injin Motar ya tsaya, mutum biyu daga cikin maharan suka fito daga cikin motar suka ƙona ta gabanin su kama gabansu."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari, Sun Kashe Mai Anguwa da Wasu Mutune a Jihar Arewa

Duk wani yunkurin jin ta bakin kakakin hukumar yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe, bai kai ga nasara ba domin ba ya ɗaga kiran waya ko amsa sakonnin da aka tura masa kan lamarin.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Sakateriyar Karamar Hukuma, Sun Yi Kazamar Barna

Miyagun 'yan bindiga sun bi dare, sun cinna wa wani sashin ƙaramar hukumar Ezza ta arewa a jihar Ebonyi, kudu maso gabashin Najeriya.

Shugaban ƙaramar hukumar, Chief Ogodo Ali Nomeh, ya ce maharan sun lalata muhimman abubuwa da suka kai darajar miliyoyin Naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel