2023: Daruruwan 'Ya'Yan APC a Mazabar Gwamnan Arewa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa daruruwan 'ya'yanta a jihar Kwara gabannin zaben 2023
- Masu sauya shekar daga jam'iyyar mai mulki a gudunmar Adewole da ke karamar hukumar Ilorin ta yamma sun koma PDP
- Sun zargi gwamnatin APC a jihar karkashin Gwamna Abdulrazaq da rashin shugabanci mai kyau
Kwara - Gabannin zaben 2023, daruruwan mambobin jam’iyyar APC a gudunmar Adewole a karamar hukumar Ilorin ta yamma a jihar Kwara sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Gudunmar itace mazabar gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq.
A wajen taron tarbarsu, ,asu sauya shekar sun kona tsintsiyarsu sannan suka yi amfani da lema wajen rufe kawunansu, jaridar Thisday ta rahoto.
Hakazalika, an samu wasu da suka sauya sheka daga yankunan Idigba, Sakele, Adeta, Idi-ope, Oke-Are, Isale-jagun, Esinrogunjo, Apalara da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ci gaban ba zai rasa nasaba da abubuwan da suka faru ba gabannin zaben jihar mai zuwa.
Shugaban masu sauya shekar, Mallam Sulaiman Alikinla ya zargi gwamnatin APC a jihar karkashin Gwamna Abdulrazaq da rashin shugabanci mai kyau.
Ya bayyana cewa, APC ta gaza cika taken ‘ya isa haka’ da ya kawo ta kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2019.
Ya kara da cewar gwamnatin APC bata isar da manufofin da ake yi tsammanin samu daga gareta ba.
Alikinla ya kuma jadadda cewa yana da matukar muhimmanci a bi salsalar duk wani mutum da ke neman mukamin siyasa yayin da ake gab da zaben 2023.
Ya kara da cewa:
“Yana da matukar muhimmanci mu yiwa Alhaji Shuaib Yaman Abdullah, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP aiki domin ya ja ragamar al’amuran jihar nan da kuma tabbatar da nasarar dukkanin yan takarar PDP a fadin kasar nan.”
A nashi jawabin, shugaban PDP a gudunmar Adewole, Alhaji Daud Akesola, ya jinjinawa karfin gwiwar masu sauya shekar na yin watsi da jam’iyya mai ci zuwa mai adawa.
Ya ce:
“Ina addu’an Allah madaukakin sarki ya albarkaci tafiyarku.”
Ya kara da cewar masu sauya shekar sun zama ‘ya’yan jam’iyyar daga matakin farko sannan ya umurcesu da suyi amfani da karfinsu a zaben 2023 don ganin dukkanin yan takarar PDP sun cimma nasara.
Na Hannun Daman Dankwanbo da Wasu Jiga-Jigan PDP 4 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Gombe
A wani labarin kuma, mun ji cewa Alhaji Ahmed Abubakar Walama, na hannun daman tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Walama ya rike mukamin kwamishinan karamar hukuma da harkokin sarauna karkashin gwamnatin Dankwambo daga 2011 zuwa 2019.
Hakazalika wani kwamishina a mulkin Dankwambo na biyu, Sa’idu Kawuwa Malala, shima ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Asali: Legit.ng