Gwamna Wike Ya Ja Tawaga Zuwa Landan, Zasu Gana Kan Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

Gwamna Wike Ya Ja Tawaga Zuwa Landan, Zasu Gana Kan Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

  • Yayin da PDP ta buɗe kamfen ɗin Atiku a Uyo, gwamna Wike ya shirya zama da yan tawagarsa a birnin Landan ranar Alhamis
  • Ana ganin Wike da sauran gwamnoni hudu dake goyon bayansa zasu tattauna kan batutuwan da suka shafi zaɓen 2023
  • Tsagin gwamnan Ribas sun tsaya tsayin daka kan bukatarsu ta sauke shugaban PDP na ƙasa daga kujerarsa

Gwamnonin jam'iyyar PDP da suka nuna fushinsu karkashin jagorancin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas za su gana yau Alhamis a birnin Landan na ƙasar Burtaniya.

Jaridar Punch ta tattaro cewa a baya gwamnonin sun tsame kansu daga tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na PDP saboda rashin cika bukatarsu.

Gwamna Nyesom Wike da Atiku Abubakar.
Gwamna Wike Ya Ja Tawaga Zuwa Landan, Zasu Gana Kan Wanda Zasu Goyi Baya a 2023 Hoto: punchng
Asali: UGC

Gwamna Wike, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abiya, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da Samuel Ortom na jihar Benuwai sun jaddada cewa tilas shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus.

Kara karanta wannan

An Samu Sabon Cigaba da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Jam'iyyar PDP Ta Ɗage Yakin Neman Zaɓe

Haka zalika, matakin Atiku Abubakar na zaɓo Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa ya ƙara tunzura Wike.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A watan Satumba da ya gabata, Wike, Makinde, da Ortom sun gana a Landan kuma taron yau ana tsammanin zasu ɗauki wasu matakai game da babban zaɓen 2023.

Bayanai sun nuna cewa matakin da PDP, Atiku suka ɗauka na ci gaba da harkokin Kamfe ba tare da Wike da sauran 'yan tawagarsa shi ne haddasa shirya wannan taron a Landan.

Kokarin sasanta Atiku da Wike

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a halin da ake ciki yanzu, duk wani yunkuri da faɗi tashin warware rikicin Atiku da gwamna Wike bai kai ga nasara ba.

Kwamitin amintattu (BoT) bisa jagorancin muƙaddashin shugaba, Sanata Adolphus Wabara, ya kafa kwamitin sasanci da zai shiga tsakani amma har yau ya gaza samar da masalaha kamar yadda ake tsammani.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Dake Takun Saka da Atiku Ya Fadi Wanda Yake Wa Kamfen Shugaban Kasa a 2023

Wike ya sha alwashin zai zauna a cikin jam'iyyar PDP, kana ya yi alkawarin ba ruwnasa da kamfen shugaban ƙasa har sai Ayu ya yi murabus.

A wani labarin kuma Kungiyar Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a Kano da Wasu Jihohi 18 Ta Juya Masa Baya

Wata ƙungiyar magoya bayan Atiku Abubakar a Kano ta sanar da janye wa daga goyon bayan ɗan takarar na PDP

Shugaban kungiyar yace mutane sama da Miliyan biyu daga jihohin arewa da Abuja sun ce ba zasu ci gaba da mara wa Atiku baya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262