Rikici Ya Kara Kamari Tsakanin Atiku da Wike, PDP Ta Dage Yakin Neman Zaben 2023
- Jam'iyyar PDP ta dakatar da yakin neman zaɓen shugaban ƙasa saboda danbarwar Atiku da gwamna Wike
- Atiku ya sake naɗa wata tawaga ta mutum uku masu faɗa aji a PDP da zasu shiga tsakaninsa da Wike don lalubo hanyar sulhu
- Sakamakon haka PDP ta tsayar da shirin gangamin Kebbi, Zamfara da jihar Kaduna don ba mutanen isasshen lokaci
Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ɗage yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na wani ɗan lokaci saboda takun sakar da aka jima ana yi tsakanin Atiku Abubakar, Gwamna Nyesom Wike.
The Nation ta tattaro cewa an ɗage Kamfen ne bisa alfarmar Atiku, wanda majiya daga jam'iyyar tace ya haɗa fitattun jiga-jigan PDP da zasu shiga tsakaninsa da gwamnan jihar Ribas.
Bayanai sun nuna cewa Atiku ya zakulo tsohon shugaban majalisar Dattawa, David Mark, tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili, da tsohon gwamnan Delta, James Ibori, a matsayin masu sulhunta tsakani.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa jam'iyyar PDP ta ɗage kamfe ne domin baiwa jiga-jigan uku damar gudanar da aikin da aka ɗora musu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
PDP ta sauya ranakun gangami a jihohi uku
A halin yanzu, gangamin taron yakin neman zaben da aka shirya gudanarwa a jihar Kebbi ranar Laraba 12 ga watan Oktoba, 2022 an soke shi.
Bugu da kari, gangamin kamfen da aka tsara gudanarwa a Zamfara ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoba da na jihar Kaduna, ranar 15 ga watan Oktoba duk an sauya lokutan.
Ɗaya daga cikin masu magana da yawun kwamitin kamfen PDP, Kola Ologbondiyan, ya tabbatar da soke gangamim yakin neman zaɓe a jihohin uku.
Ologbondiyan ya bayyan cewa taron da aka shirya gudanarwa a Kaduna ranar Jumu'a an matsar da shi zuwa ranar Litinin 17 ga watan Oktoba, 2022. Bai faɗi ranakun na Zamfara da Kebbi ba.
A ranar 10 ga watan Oktoba, PDP ta bude fagen kamfe a Uyo, jihar Akwai Ibom, sai dai gwamnoni 5 daga cikin 13 na PDP ba su halarci wurin ba.
A wani labarin kuma Masu Yakin Neman Zaben Atiku a Kano da Wasu Jihohi 18 Sun Juya Masa Baya
Wata ƙungiyar magoya bayan Atiku Abubakar a Kano ta sanar da janye wa daga goyon bayan ɗan takarar na PDP.
Shugaban kungiyar yace mutane sama da Miliyan biyu daga jihohin arewa da Abuja sun ce ba zasu ci gaba da mara wa Atiku baya ba.
Asali: Legit.ng