Jam'iyyar LP Ta Fitar Sunayen Mambobi 1,234 Na Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa, Babu Jiga-Jigai 2
- Jam'iyyar LP ta fitar da jerin sunayen mambobi 1,234 na tawagar yakin neman zabenta na shugaban kasa
- Ba a ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Peter Obi da abokin takararsa, Baba-Ahmed a taron kaddamar da kwamitin ba
- Taron wanda aka gudanar a Abuja a yau Laraba, ya samu halartan magoya bayan yan takarar da dama
Abuja - Jam’iyyar Labour Party (LP) ta fitar da jerin sunayen ‘ya’yan kwamitin yakin neman zabenta na shugaban kasa a zaben 2023.
Premium Times ta rahoto cewa an gabatar da sunayen mutanen su 1,234 a wani taro da aka shirya a Abuja a ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba.
Koda dai an yi masa lakabi da “Taron Manema Labarai na kafin Kamfen”, taron ya samu halartan magoya bayan yan takarar jam’iyyar da dama.
Sai dai kuma, daga Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar har abokin takararsa, Yusuf Baba-Ahmed, basu halarci taron ba, rahoton The Guardian.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Obi ya yi wata wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya tabbatar da cewar yana halartan taron ICAN karo na 52.
An Nemi ‘Dan Tsohon Shugaban Najeriya ya zama Mataimakin Peter Obi, Ya ki Yarda
A wani labarin, mun ji cewa tsohon mataimakin Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari ya bada labarin yadda suka yi da mutanen Peter Obi na jam’iyyar LP.
Da aka yi hira da shi a wani shiri na siyasa a gidan talabijin Channels, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari yace an tuntube shi a kan maganar takara.
'Tsohon Ministan yake cewa bai karbi tayin da aka yi masa na zama abokin takarar Obi a zaben shugaban kasa a karkashin LP ba saboda wasu dalilai.
Asali: Legit.ng