An Nemi ‘Dan Tsohon Shugaban Najeriya ya zama Mataimakin Peter Obi, Ya ki Yarda

An Nemi ‘Dan Tsohon Shugaban Najeriya ya zama Mataimakin Peter Obi, Ya ki Yarda

  • Alhaji Mukhtar Shehu Shagari ya yi ikirarin Jam’iyyar LP ta tuntube shi a kan batun takara tare da Peter Obi
  • ‘Dan siyasar yace an nemi ya zama abokin takaran Peter Obi a zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar 2023
  • Tsohon mataimakin Gwamnan na jihar Sokoto bai karbi wannan tayin ba, yana ganin PDP ba sa’ar LP ba ce

Abuja - Tsohon mataimakin Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari ya bada labarin yadda suka yi da mutanen Peter Obi na jam’iyyar LP.

Da aka yi hira da shi a wani shiri na siyasa a gidan talabijin Channels, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari yace an tuntube shi a kan maganar takara.

Tsohon Ministan yake cewa bai karbi tayin da aka yi masa na zama abokin takarar Obi a zaben shugaban kasa a karkashin LP ba saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

Legit.ng Hausa ta fahimci an tattauna da wasu manyan ‘yan siyasar Arewa wajen zakulo wanda zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a LP.

PDP ba sa'ar LP ba ce - Mukhtar Shehu Shagari

Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto, Mukhtar Shehu Shagari yana ganin babu yadda za ayi jam’iyyar LP ta doke PDP, don haka ya ki karbar tayin na su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shagari wanda mahaifinsa ya yi shugabancin Najeriya tsakanin 1979 da 1983, ya jefawa ‘ya ‘yan LP tambayoyin da bai iya samun gamsassun amsoshi ba.

Mukhtar Shehu Shagari
Mukhtar Shehu Shagari CFR Hoto: @mukhtarshagari
Asali: Twitter

“An tuntube ni domin zama abokin takarar Peter Obi. Na fada masu ba zan iya barin jam’iyyata ba, saboda nayi imani da manufarta.
Na gamsu da jam’iyya da abin da ta tsaya a kai a Najeriya, kuma nayi imani Labour Party ba za ta iya doke mu a kowane irin zabe ba.

Kara karanta wannan

Amaechi, da ‘Yan APC 10 da Suka Nemi Takaran 2023, Amma Aka Daina Jin Duriyarsu

Na tambayi ‘yan jam’iyyar LP da suka tuntube ni, wanene shugaban jam’iyyar a Sokoto? Su wanene ‘yan takarar LP a jihar Sokoto?
Wanene ke takarar Sanata? Wanene yake neman takarar Gwamna da sauransu. Ban samu amsa ba.” - Mukhtar Shehu Shagari.

‘Dan siyasar yana kuma ganin ‘dan takaran na jam’iyyar LP ba zai iya magance matsalolin rashin tsaro, talauci da sauran abubuwa da suka addabi kasar ba.

'Yan takara sun yi kusufi

Ga shi an shiga kamfe a Najeriya, amma kun samu rahoto cewa wasu da aka gwabza da su wajen yakin tikitin Jam’iyyar APC sun zama ‘yan bayan fage a 2023.

Rotimi Amaechi wanda ya yaki Bola Tinubu a zaben fitar da gwani ya rasa takara da kujera a gwamnati, kuma an fita batunsa yanzu a tafiyar siyasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng