‘Dan Takaran da Ya Janyewa Tinubu a Zaben Gwani Ya Sha Alwashin Zai Yaki a APC

‘Dan Takaran da Ya Janyewa Tinubu a Zaben Gwani Ya Sha Alwashin Zai Yaki a APC

  • Tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun yace ba zai marawa jam’iyyar APC baya a zaben 2023 ba
  • A zaben Shugaban kasa, Sanatan Ogun ta tsakiya yana goyon bayan Bola Tinubu 100% bisa 100%
  • A zaben gwamnan jiha da za ayi a 2023, Sanata Ibikunle Amosun zai sake yakar Dapo Abiodun

Ogun - Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya fito karara yana cewa ba zai marawa jam’iyyar APC a zaben gwamna da za ayi a 2023 ba.

A rahoton da muka samu daga Daily Trust a ranar Litinin, Sanata Ibikunle Amosun yace zai goyi bayan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Sanatan yana goyon bayan Biyi Otegbeye mai takara a jam’iyyar hamayya ta ADC ya karbi mulki daga hannun Gwamna Abiodun mai neman ya zarce.

Kara karanta wannan

Amaechi, da ‘Yan APC 10 da Suka Nemi Takaran 2023, Amma Aka Daina Jin Duriyarsu

Amma kuma a zaben shugabancin Najeriya, Amosun yana cikin manyan magoyon bayan ‘dan takaran jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu.

A zaben kujerar gwamna ne kurum ‘dan siyasar zai yaki jam’iyyarsa. Jigon na APC zai bada gudumuwa wajen ganin Tinubu ya zama shugaban kasa.

Jaridar nan ta Daily Post tace hakan ya tabbatar da cewa Amosun zai sake yin adawa ga Gwamna Dapo Abiodun wanda ya mikawa mulki a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanatan APC, Amosun
Ibikunle Amosun da Bola Tinubu Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ba na kan layin APC a Ogun - Amosun

Amosun ya yi hira da BBC Yoruba a Abeokuta yace a zaben gwamna bai tare da jam’iyyarsa, amma yana tare da Tinubu sau da kafa a zaben kasa.

“Ba na boye-boye. Shiyasa mutane ke cewa ka da ka ce haka. A zaben gwamna, ni da mutanena ba mu a kan wannan layin.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

“Biyi Otegbeye ne wanda nake goyon baya, kuma ADC ita ce jam’iyyar.”

- Ibikunle Amosun

Ina maganar Adekunle Akinlade?

A zaben 2019, a lokacin yana shirin barin gadon mulki, Amosun ya ki goyon bayan wanda jam’iyyarsa ta ba tikiti, sai ya dauko Adekunle Akinlade.

Adekunle Akinlade ya yi takara ne a inuwar jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM). Ana zargin yanzu an samu sabani tsakanin ‘yan siyasar.

Abiodun ya zama Gwamna ne da kuri’u 241,670, ya doke Akinlade wanda ya tashi da 222,153. An ji labari Amosun yace da murdiya APC ta ci zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng