2023: Kusoshin Kiristocin Jam’iyya Za Su yi Taron Dangi Domin Dankara Tinubu da Kasa
- Da alama dai Kiristocin Arewa na Jam’iyyar APC sun yi watsi da Bola Tinubu a zaben shugaban kasa
- Jagororin APC sun ce sam bai kamata a tsaida Musulmi da Musulmi a takarar shugabancin Najeriya ba
- Rt. Hon. Yakubu Dogara ne ya jagoranci abokan tafiyarsa zuwa wani taro da aka yi har da Musulmai
Abuja - Tasirin addini a wajen zaben shugaban kasa zai iya jawowa jam’iyyar APC illa yayin da take neman zarcewa a kan mulkin Najeriya.
Wani rahoto da muka samu daga Punch a ranar Litinin 10 ga watan Oktoba 2022, ya nuna kiristocin jam’iyyar APC za su yaki takarar Bola Tinubu.
Jagororin Kirista da ke APC sun amince za su marawa wani ‘dan takaran shugaban kasa daya baya domin ya yaki tikitin Musulmi da Musulmi.
Tsohon shugaban majalisa, Rt. Hon. Yakubu Dogara da kuma Babachir David Lawal suke jagorantar kiristocin Arewa da ke cikin jam’iyyar APC.
A karshen taron da mabiya addinin kiristan na yankin Arewacin Najeriya a APC suka yi, sun cin ma matsaya za su dage kan hada-kan jama'a.
A zaman da aka yi, sun nemi a daina tabo abin da za su jawo a soki addini da sunan siyasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An sa hannu a takardar bayan taro
Dogara da tsohon Ministan harkokin ruwa na gwamnatin Obasanjo watau Mukhari Shagari suka sa hannu a kan takardar da aka fitar bayan taron.
Sauran wadanda suka halarci wannan taro sun hada da Boni Haruna, Abdulfattah Ahmed da su Damishi Sango, Yomi Awoniyi da Simon Achuba.
“Kiristocin Arewacin Najeriya a jam’iyyar APC sun hadu da wasu ‘yanuwansu Musulmai daga Abuja da jihohi 19 na Arewa, kuma sun amince da:
Mun yarda za muyi aiki tare domin kawo zaman lafiya, hadin-kai da kwanciyar hankali.
Muyi aiki da juna, mu goyi bayan wata jam’iyya mai kishin kasa da za ta jawo hadin-kai da tafiya da kowa, da ba duka ‘yan kasa damar ayi tafiya da su.”
- Yarjejeniyar bayan taro
A karshe rahoton yace taron ya soki tikitin Musulmi da Musulmi da APC tayi domin zaii ya raba kan jama’a a kasa irin Najeriya mai mutane iri-iri.
Muna magana da wasu jam'iyyu
Kuna da labari Babachir David Lawal wanda ya rike sakataren gwamnatin tarayya ya raba jiha da Tinubu saboda ya zabo musulmi, Kashim Shettima.
Kwanaki Injiniya Babachir David Lawal ya shaidawa ‘yan jarida magana tayi nisa tsakaninsu da PDP, LP da kuma NNPP a kan batun siyasar 2023.
Asali: Legit.ng