2023: Atiku Ne Kadai Ya Shirya Shugabancin Najeriya, Kakakin Kamfen PDP
- Mai magana da yawun tawagar kamfen shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Charles Aniagwu. yace Atiku ne kadai ya shirya shugabancin Najeriya
- Aniagwu, wanda kwamishina ne a jihar Delta yace sauran masu neman zama shugaban kasa ba su da shirin ceto Najeriya kamar na Atiku
- Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC da Peter Obi na Labour Party na cikin manyan yan takarar da zasu gwabza da Atiku a zaben 2023
Abuja - Mista Charles Aniagwu, kakakin tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na PDP, yace Atiku Abubakar ne ɗan takara ɗaya tilo da ya shirya jagorantar Najeriya.
Aniagwu, wanda ke matsayin kwamishinan yaɗa labarai a jihar Delta, ya yi wannan furucin ne a wata hira kafar Talabijin ta Arise ranar Asabar.
Yace tsawon shekaru 7 da suka shuɗe, jam'iyyar APC mai mulki ta gurgunta tattalin arzikin ƙasa, ilimi, tsaro da kuma haɗin kai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mista Aniagwu, yace Atiku ya shirya zai ƙarfafa ɓangaren masu zaman kansu domin su ja ragamar tattalin arzikin ƙasa ta yadda mutane zasu samu ayyukan yi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace, "Ko ɗaya APC bata da wani shirin cigaban ƙasar nan, idan kuma akwai ta ya suke kokarin aiwatar da su? Da ace suna da wani tsari mai kyau da Najeriya ba ta tsinci kanta a yanayin nan ba."
"'Yan Najeriya ne suka ɗora su kan madafun iko a 2015 amma suka watsar da su bayan gaza cika alƙawurran da suka ɗauka wurin kamfe. Shirin da Atiku ke da shi na kowa ne kuma ɗan takararmu da Okowa sun fahimci matsalolin."
"Ba wai haka nan aka wayi gari Atiku ya ayyana shiga takara ba, tun tuni yake shiri tsawon lokaci kuma ya gamsar da abinda ake bukata don ceto Najeriya da sake ginata."
Wane ɗan takara ne ya shirya jagorantar Najeriya?
"Atiku ne kaɗai ɗan takarar da ya shirya tsaf don jagorantar Najeriya, sauran masu nema sam ba su shirya ba. Duk lokacin daka tambayi masu son zama shugaban ƙasa za su ce maka suna gab da ayyan kudurorinsu, hakan na nufin ba su shirya ba."
"Najeriya ta kai matakin da take buƙatar kula ta gaggawa kuma ba'a bukatar wani shugaba da bai shirya tsamo ƙasar nan daga ƙalubalen da take ciki ba sakamakon gazawar gwamnatin APC."
- Charles Aniagwu
Bugu da ƙari, ya bayyana cewa Atiku yana da shiri a ƙasa na kawo ƙarshen waɗannan matsalolin da banbance-banbancen da ake samu tsakanin al'umma.
A wani labarin kuma Gwamnan Arewa Ya Umarci Ciyamomi 20, Mataimaka da Wasu Kusoshin Gwamnati Su Sauka Daga Kujerunsu
Gwamna Bala Muhammed na Bauchi ya umarci Ciyamomi 20 su sauka daga kujerunsu bayan wa'adinsu ya ƙare.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar, umarnin ya shafi mataimakan ciyamomi, Sakatarori da Kansiloli.
Asali: Legit.ng