Ka Yi Murabus Ko Ka Bayar Da Hakuri, Gwamna Ortom Ga Shugaban PDP Na Kasa

Ka Yi Murabus Ko Ka Bayar Da Hakuri, Gwamna Ortom Ga Shugaban PDP Na Kasa

  • Gwamnan jihar Benuwai ya yi kira ga shugaban PDP, Iyorchia Ayu, ya yi murabus kamar yadda ya alƙawarta a baya
  • Samuel Ortom, gwamnan jihar da Ayu ya fito a arewa ta tsakiya, yace Ayu ya faɗa wa duniya a baya cewa zai sauka idan aka tsayar da ɗan arewa
  • Gwamna Ortom ya shawarci Ayu ya ba da haƙuri idan ba zai sauka ba amma ba ya dinga cewa zangon mulkinsa na shekara huɗu bane

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya yi kira ga shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga kan kujerarsa ko kuma ya ba da hakuri.

Jaridar The Nation ta ce wannan shi ne karo na farko da Ortom, gwamnan jihar da Ayu ya fito daga arewacin Najeriya, ya nemi da ya sauka daga kan mukamin shugaban PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.
Ka Yi Murabus Ko Ka Bayar Da Hakuri, Gwamna Ortom Ga Shugaban PDP Na Kasa Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Tawagar wasu gwamnoni karkashin jagorancin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sun matsa lamba suna kira ga shugaban PDP ya yi murabus domin dan kudu ya maye gurbinsa.

A cewarsu cika wannan sharadin ne kadai zai sa su goya wa dan takarar shugabam kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, baya a zaben 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi a wurin taron majalisar zartaswa a gidan gwamnatinsa da ke Makurdi a karshen makon nan, gwamna Ortom ya hakaito yadda Ayu ya yi alkwarin yin murabus idan dan arewa ya lashe tikitin takarar PDP.

Alƙawarin da Ayu ya ɗauka a baya

Ortom, wanda ke cikin tawagar gwamnonin tsagin Wike, ya roki Ayu ya nuna halin dattako ta hanyar cika alkawarin da ya dauka na yin murabus.

A kalamansa gwamnan yace:

Kara karanta wannan

Ba harka: Dan takarar shugaban kasan wata jam'iyya ya tsorata, zai janye daga takara

"Ayu ya fada wa duniya cewa idan har ɗan arewa ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP to zai yi murabus daga mukamin shugaban jam'iyya.
"Idan kuma baka son yin murabus to ka nemi afuwa amma ba zai yuwu kace sai ka ƙare zangon shekara huɗu ba don haka ba zaka yi murabus kamar yadda harshenka ya faɗa a baya ba."

A wani labarin kuma Shugabannin APC 16 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Sakkwato Gabanin 2023

Yayin da 'ya'yan jam'iyyar APC ke murnar dawowar Bola Tinubu, jam'iyyar ta yi rashin wasu shugabanninta na matakin gunduma a Sakkwato.

Wasu shugabannin APC a gundumomi biyu dake karamar hukumar Sabon Birni sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262