2023: Tsohon Ministan Buhari Ya Gabatar Da Hujja, Ya Shigar Da Kara Don Soke Takarar Tinubu, Atiku
- An kallubalanci takarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC da takwararsa Atiku Abubakar na jam'iyyar 2023 a babban kotun tarayya na Abuja
- An tattaro cewa tsohon karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiubu, ya shigar da kara a kotu a ranar Juma'a, 30 ga watan Satumba
- Nwajiubu ya shaidawa kotu ta soke nasarar da Atiku da Tinubu suka samu yayin zabukan cikin gida na PDP da APC kan zargin siyan kuri'u
Abuja - An yi kira ga babban kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Juma'a 30, ta soke takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
A cewar The Cable, tsohon karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya shigar da karar a kotun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Zargin siyan kuri'u da Tinubu ya yi yayin zaben fidda gwani na APC
A kararsa, Nwajiuba ya ce Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya saba dokokin zabe yayin zaben cikin gida na jam'iyyar.
Tsohon ministan, ta hannun lauyansa, Okere Nnamdi, ya shaidawa kotu cewa an tafka magudi a zaben cikin gidan da Tinubu ya yi nasarar, har ma Rotimi Amaechi (tsohon ministan sufuri) ya koka cewa mafi yawancin daliget din sun sayar da kuri'unsu.
Domin gabatar da hujja kan zarginsa, Nwajiuba ya gabatarwa kotun faifan bidiyo inda Amaechi ke kokawa kan sayan kuri'un.
An sake tambaya kan takardun karatun Tinubu, da tushen arzikinsa
Har wa yau, mai shigar da karan ya taso da batun takardun karatun tsoho gwamnan na Jihar Legas da tushen arzikinsa.
Nwajiuba ya na son kotun ta tabbatar da cewa Tinubu "wanda a baya ya gabatar da takardar rantsuwa ga INEC cewa takardar karatun firamarinsa da sakandare sun bace, ba zai iya zuwa daga baya ya musanta hakan ba."
Lauyan ya gabartawa kotu takardun rantsuwa da Tinubu mai dauke da sa hannunsa lokacin zai yi takarar gwamnan karkashin jam'iyyar AD.
Zaben shugaban kasar 2023: Karar Nwajiuba kan Atiku
Karar ta kuma bukaci a soke takarar Atiku Abubakar, dan takarar PDP, kan saba dokar zabe.
Sauran wadanda aka yi karar sun hada da APC, PDP, AGF Abubakar Malami, da INEC.
Ya yi ikirarin cewa Atiku shima ya siya kuri'u kamar Tinubu, mai karar ya roki kotun ta tantace ko "abin da wadanda aka yi kararsu na 3 da 4 (Tinubu da Atiku) da wakilansu, wadanda suka siya kuri'u da dallolin Amurka, wanda kudin waje ne kuma ba halastacce a Najeriya ba karkashin dokar CBN Act, da mallakarsa da ke bukatar a sanar karkashin dokar EFCC Act, aka yi amfani da su wurin siyan kuri'u don amfanin wanda aka yi karar na 3 da 4, na nufin kuri'un da suka samu ba su halasta ba, kuma hakan na nufin ba za su amfana da haramtaccen abin da suka aikata ba."
Bayan sauraron karar, alkalin kotun, Mai sharia Inyang Ekwo, ya bukaci a tattara dukkan bayanan da mai karan ya shigar.
Amma, Mai sharia Ekwo kuma ya dage cigaba da shari'ar zuwa 6 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng