Kola Abiola Na Jam'iyyar PDP Shirin Janyewa Daga Takarar Shugaban Kasa a 2023

Kola Abiola Na Jam'iyyar PDP Shirin Janyewa Daga Takarar Shugaban Kasa a 2023

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PRP na iya janyewa daga takara a kowane lokaci daga yanzu saboda wasu dalilai
  • Jam'iyyun siyasa a Najeriya sun fara gangamin tallata 'yan takararsu gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa
  • An samu tsaiko a PRP yayin da daya daga cikin 'yan takarar da suka gwabza a zaben fidda gwani ta tado da sabon batu

Akwai yiwuwar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PRP, Kola Abiola ya bayyana janyewa daga takarar shugaban kasa a kowan lokaci daga yanzu, inji rahoton jaridar Indenpendent.

Kola, wanda da ne ga jigon siyasar nan na Najeriya marigayi Bashorun M.K.O. Abiola ya lashe zaben fidda gwanin da jam'iyyar PRP ta gudanar a watan Yuni.

M.K.O Abiola ne ya lashe zaben watan Yunin 1993.

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

Akwai yiwuwar Kola Abiola ya janye daga takara
Kola Abiola Na Jam'iyyar PDP Shirin Janyewa Daga Takarar Shugaban Kasa a 2023 | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Da yake zantawa da wakilin jaridar, wani jigon PRP da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, dan takarar nasu ya yi tunanin cewa, a matsayinsa na matashi, matasan Najeriya za su yi shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, ya yi tunanin dattawan Yarbawa za su bashi hadin kai, musamman abokan mahaifinsa da ya rasu, amma abin bai samu ba.

A cewar majiyar, Kola ya duba da yadda Bola Ahmad Tinubu na APC dsa Peter Obi na LP ke kara karbuwa a kasar, don haka yake tunanin janyewa daga takarar, haka nan Legit.ng ta tattaro.

Kola zai goyi bayan Tinubu ko Atiku

Majiyar ta kuma bayyana cewa, akwai yiwuwar Kola ya yi kira ga magoya bayansa da su marawa daga daga cikin 'yan takarar jam'iyyun da suka fi karbuwa a kasar.

A cewar majiyar:

Kara karanta wannan

2023: Mata a yankin su Peter Obi sun yi biris dashi, sun yi gangamin nuna kaunar Tinubu

"Ya yi tunanin zai tabuka abin kirki ganin soyayyar da 'yan Najeriya ke yiwa mahaifinsa da kuma duba da cewa za a yi zaben ne shekaru 30 bayan zaben 12 ga watan Yunin 1993.
"Sai dai, ina ganin burin Asiwaju Bola Tinubu wanda ya samu karbuwa a Kudu maso Yamma da Peter Obi da yake da tarun matasa zai sa ya sake tunani.
"Abubuwa ba sa tafiya kamar yadda yake tsammani kuma akwai yiwuwar ya janye daga takarar nan kusa. Har yanzu dai muna jiran hukuncinsa na zai yanje yanzu ko zai ayyana goyon baya ga dan takarar da ya fi karbuwa a ranar zabe."

A makon nan dama daya daga cikin 'yan takarar da suka gwabza a zaben fidda gwanin PRP, Mrs Patience Ndidi Key ta bayyana cewa, ita tafi cancanta da lashe zaben, Tribune Online ta ruwaito.

Ta bayyana kokawarta da cewa, an yi makudi a zaben fidda gwanin da aka gudanar a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Allah Ne Ya Turo Tinubu Ya Cece Mu, Jigon APC Ya Hango Alherin Dan Takararsu

A wani labarin, Obidike Chukwuebuka, mamba a jam'yyar APC ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, zaben 2023 mai zuwa zai zo da sauyi mai yawa idan aka zabi Asiwaju Bola Tinubu.

Obidike, wanda kuma shine darakta janar na tawagar gangamin nuna goyon bayan APC ya bayyana wannan batun ne a jiya Alhamis 6 ga watan Oktoba, kamar yadda ya turowa Legit.ng a wata sanarwa.

A cewarsa, Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ne macecin da Allah ya turo ya tsamo Najeriya daga halin kakani-kayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.