Atiku Ya Nada Jigo A PDP Matsayin Kakakin Kwamitin Kamfen Dinsa A Zaben 2023

Atiku Ya Nada Jigo A PDP Matsayin Kakakin Kwamitin Kamfen Dinsa A Zaben 2023

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya nada Kolawole Ologbondiyan matsayin kakakin kamfen dinsa
  • Mr Paul Ibe, mashawarcin Atiku kan kafofin watsa labarai ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Ologbondiyan, shine sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar PDP daga Disambar 2017 zuwa Disambar 2021 kuma mamba ne a NEC

FCT - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nada Kolawole Stephen Ologbondiyan, tsohon sakataren watsa labaran kasa na PDP, a matsayin daya cikin kakakin kamfen dinsa 2023.

Ologbondiyan
Atiku Ya Nada Jigo A PDP Matsayin Kakakin Kwamitin Kamfen Dinsa A Zaben 2023. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Facebook

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Paul Ibe, mashawarcin Atiku kan kafofin watsa labarai, da Tribune Online ta samu ya ce nadin ya fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

A karon farko: Diyar Atiku ta fito a jerin matasan da za su yi yawon kamfen din PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da wannan nadin, Ologbondiyan ya shiga jerin wasu masu magana da yawun kamfen din da Atiku ya nada tunda farko don su rika tallata shi ga masu zabe.

Takaitaccen tarihin ayyukan Ologbondiyan

Ologbondiyan, shine sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar PDP daga Disambar 2017 zuwa Disambar 2021.

Shine kuma direktan bangaren watsa labarai na kwamitin kamfen din takarar shugaban kasa na PDP a zaben shekarar 2019 kuma yanzu mamba na kwamitin NEC a jam'iyyar.

Kuma shine mashawarci na musamman ka bangaren watsa labarai ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark daga 2007 zuwa 2015.

Ologbondiyan, kwararren dan jarida ne, ya fara aiki daga kasa har ya kai babban matsayi, daga mai tantance labarai zuwa editan shirye-shirye ya zama mataimakin editan siyasa, editan siyasa a jaridar Thisday Newspaper.

Atiku Ya Nada Saraki, Shekarau da Wasu Jiga-Jigan PDP a Wasu Muhimman Mukamai

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

A bangare guda, yayin da ake shirin fara kamfe na zaɓen 2023, mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya yi sabbin naɗe-naɗe masu muhimmanci da nufin karfafa tawagar yaƙin neman zaɓensa.

Channels TV ta ruwaito cewa waɗanda Atiku ya naɗa sun haɗa da, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a matsayin wakilin ɗan takarar na musamman da Sanata Pius Anyim, a mukamin mashawarci na musamman.

Sauran waɗanda suka samu shiga a matsayin mashawarta na musamman sune, tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola da kuma Sanata Ehigie Uzamere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel