Ana Sauraron Dawowar Bola Tinubu Najeriya a Yau Dinnan Inji Hadimin Buhari
- Babu mamaki nan ba da dadewa ba a ji labari ‘Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu ya shigo Najeriya
- Bashir Ahmaad yace a yau ake sa ran dawowar Bola Tinubu mai neman takaran APC a zabe mai zuwa
- Matashin yana cikin ‘yan kwamitin da ke yi wa jam’iyyar APC yakin neman zaben Shugaban kasa
Abuja - Asiwaju Bola Tinubu mai neman takarar shugabancin kasa a inuwar jam’iyyar APC mai mulki ya shirya dawowa Najeriya.
Idan maganar da Bashir Ahmaad ya yi ta tabbata to, a yau ne Asiwaju Bola Tinubu zai duro Najeriya bayan ‘yan kwanaki yana Birtaniya.
Hadimin shugaban Najeriyan ya yi wannan bayani a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.
Da karfe 3:19 na yamma, Bashir Ahmaad ya yi magana a dandalin sada zumuntan, yake cewa ‘dan takaransu na APC zai dawo gida yau.
Matashin yace hakan yana zuwa ne bayan ‘dan takaran na APC ya yi muhimman taron siyasa iri-iri da yake birnin Landan a kasar Ingila.
Baya ga cewa jirgin Asiwaju Bola Tinubu zai sauka ne a Abuja, hadiman shugaban kasar bai yi wani karin haske a maganar da ya yi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Bayan kwanaki yana tattaunawar siyasa da halartar tarurruka a Landan, ana sa ran an jima ‘dan takaranmu, Asiwaju Bola Tinubu zai sauka a Abuja.
-Bashir Ahmaad
Daily Trust ta tabbatar da wannan labari, tace dawowar tsohon gwamnan na Legas yana zuwa ne bayan ya shafe kwana 12 a kasar Turan.
Daga lokacin da ya bar Najeriya zuwa Birtaniya a ranar 26 ga watan Satumban 2022, an yi ta yada jita-jitar Tinubu yana jinya a gadon asibiti.
Mai taimakawa shugaban kasar yana cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben APC, su ne ke jagorantar sashen sadarwa na zamani a kamfe.
A rahoton da gidan talabijin na Channels TV ya fitar, an ji Festus Keyamo yana cewa bai da masaniya a kan ranar da 'dan siyasar zai dawo.
APC ta zama 'yar kallo
Kun samu labari cewa babu yadda Jam’iyyar APC ta iya da zaben Gwamna a Akwa Ibom, kuma Sha’aban Sharada ya samu tikiti a jihar Kano.
Hukumar INEC ba za ta kyale Jam’iyyar LP ta shiga zaben Ogun ba, kuma an canza mata wanda zai yi takarar Gwamna a Kaduna a zaben 2023.
Asali: Legit.ng