Babbar Kotu Ta Soke Tikitin Dan Takarar Jam'iyyar APC a Jihar Ogun

Babbar Kotu Ta Soke Tikitin Dan Takarar Jam'iyyar APC a Jihar Ogun

  • Babbar Kotun tarayya dake zama a Abeokuta ta soke takarar Ishaq Abiodun Akinlade na jam'iyyar APC a zaɓen 2023
  • Akinlade, shi ne ɗan takarar da APC ta ba tikitin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar South/Ipokia a jihar Ogun
  • Ɗaya daga cikin yan takarar da suka nemi tikitin ne ya garzaya Kotu inda ya ƙalubalenci APC, Akinlade da kuma INEC

Ogun - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, ta soke zaɓen Hon. Isiaq Abiodun Akinlade a matsayin ɗan takarar mamban majalisar dokokin tarayya mai wakiltar mazaɓar South/Ipokia.

Vanguard ta rahoto cewa Alƙalin Kotun mai shari'a O.O. Oguntoyinbo, ya ayyana tsayar da Isiaq Akinlade da jam'iyyar APC ta yi da, "saɓa wa doka, mara amfani kuma wanda aka soke."

Kara karanta wannan

Obi Ɗan-Gata: Gwamnoni 18 Ne Ke Marawa Obi Baya, Ohanaeze

Kotu ta soke tikitin APC a Ogun.
Babbar Kotu Ta Soke Tikitin Dan Takarar Jam'iyyar APC a Jihar Ogun Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kotun ta kafa hujjar cewa Akinlade bai lale kuɗi ya sayi Fam ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara, haka nan jam'iyyar APC ba ta tantance shi ba a lokacin da aka ware wa 'yan takarar majalisar tarayya.

Kotu ta umarci APC ta canza zaɓen fidda gwani a mazaɓar

Bayan haka kuma, Kotun ta umarci jam'iyyar APC ta shirya sabon zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 40 masu zuwa domin zaɓo ɗan takara a mazaɓar South/Ipokia ta tarayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika, Kotun ta haramta wa Akinlade sake neman takara a sabon zaɓen fidda gwanin da ta ba da umarnin a canza a mazaɓar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi tikitin mazaɓar, Chief Michael Adebayo, shi ne ya garzaya Kotu ya ƙalubalanci jam'iyyar APC, Isiaq Abiodun Akinlade, da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC).

Kara karanta wannan

Daga Karshe, An Faɗi Gaskiyar Halin da Bola Tinubu Ke Ciki Da Babban Abinda Yake Yi a Landan

A wani labarin na daban kuma, An Faɗi Gaskiyar Halin da Bola Tinubu Ke Ciki Da Babban Abinda Yake Yi a Landan

Jam'iyyar APC reshen ƙasar Burtaniya ta karyata jita-jitar da mutane ke yaɗa wa cewa Tinubu ya je jinya ne a Landan.

Shugaban tawagar kamfen APC na ƙasashen waje, Joseph Adebola, yace ɗan takarar nan nan cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel