Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Rashin Mambobinta, Ɗaruruwa Sun Koma PDP a Bauchi
- Kwanaki kaɗan bayan fara kamfe a hukumance, jam'iyyar PDP a jihar Bauchi ta samu gagarumin goyon baya
- Wasu dandazon mambobin APC a yankin Duguri sun tabbatar da sauya sheƙa zuwa PDP don mara wa Ƙauran Bauchi baya
- Sun ce gwamnan ya aiwatar da muhimman ayyuka a yankinsu, don haka zasu saka masa a zaɓen 2023
Bauchi - Jaridar Trubune online ta ruwaito cewa an samu tururuwar sauya sheƙar mambobin jam'iyyar APC mai adawa a jihar Bauchi zuwa jam'iyyar PDP mai mulki.
Sabbin mambobin sun samu kyakkyawar tarba da maraba zuwa jam'iyyar PDP daga babban mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin cikin gida, Abubakar Adamu Barde, a wani taro da aka shirya ƙarshen makon nan.
Hadimin gwamna Bala Muhammed da masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomin Alkaleri da Kirfi ne suka tarbi ɗaruruwan masu sauya sheƙar daga APC zuwa PDP a Duguri.
Meyasa suka yanke fice wa daga APC?
Jagororin tawagar masu sauya sheƙar sun bayyana cewa sun yanke tattara kayansu su bar APC ne domin su tallafa wa ƙoƙarin tazarcen gwamna Bala Muhammed wanda yake ɗa a wurinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsu, gwamnan ya aiwatar da muhimman ayyuka a lungu da saƙo na ƙaramar hukumarsu, da kuma yankin Duguri baki ɗaya.
Bugu da ƙari, sun sha alwashin goyon bayan jam'iyyar PDP tun daga sama har ƙasa a babban zaɓen 2023 da ke tafe.
Ɗaya daga cikin shugabannin masu sauya sheƙar, Muhammed, ya shaida wa dandazon mutanen cewa gwamna ya yi abin a zo a gani a tsawon shekaru uku da hawa madafun iko.
Bisa haka a cewarsa, "A matsayin waɗanda suka amfana da kowane fanni ya rataya a wuyansu su yi duk me yuwuwa don sauran mutane su ci gajiya nan gaba."
A wani labarin kuma Kwankwaso Ya Shiga Matsala, 'Yar Takarar Gwamnan Jiha Da Ta Lashe Tikiti Ta Fice daga NNPP
Mace ɗaya tilo da jam'iyyar NNPP ta tsayar takarar gwamna a zaɓen 2023 ta sanar da janye wa daga tseren takara.
Jackie Adunni Kassim, mai neman zama gwamnan jihar Ogun a NNPP tare da magoya bayanta sun fice daga jam'iyyar.
Asali: Legit.ng