2023: Kwankwaso Ya Shiga Matsala, 'Yar Takarar Gwamna Da Ta Lashe Tikiti Ta Fice NNPP

2023: Kwankwaso Ya Shiga Matsala, 'Yar Takarar Gwamna Da Ta Lashe Tikiti Ta Fice NNPP

  • Mace ɗaya tilo da jam'iyyar NNPP ta tsayar takarar gwamna a zaɓen 2023 ta sanar da janye wa daga tseren takara
  • Jackie Adunni Kassim, mai neman zama gwamnan jihar Ogun a NNPP tare da magoya bayanta sun fice daga jam'iyyar
  • Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan fara kamfen takarar shugaban kasa, wanda Kwankwaso ke nema a NNPP

Yayin da ake dakon INEC ta fitar da sunayen ƙarshe na yan takarar gwamna da mambobin majalisar dokokin jihohi, wata matsala ta kunno kai a jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a jihar Ogun.

Vanguard ta tattaro cewa 'yar takarar gwamnan Ogun a inuwar NNPP, Jackie Adunni Kassim, ta sanar da janye wa daga tseren bisa abinda ta kira da, "Cin amana," daga jagororin jam'iyyar reshen jihar.

Jackie Adunni Kassim.
2023: Kwankwaso Ya Shiga Matsala, 'Yar Takarar Gwamna Da Ta Lashe Tikiti Ta Fice NNPP Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Kassim, mace ɗaya tilo mai neman zama gwamna a inuwar NNPP ta sanar da matakin da ta ɗauka ne yayin da take jawabi ga magoya bayanta na faɗin jihar a wurin wani taro da ya gudana a Sango, jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Wani Gwamnan Arewa Ya Fusata, Ya Dakatar da Biyan Malaman Jami'ar Jiharsa Albashi

Yar siyasar ta ƙara da cewa babu yarda a tsakanin tafiyar magoya bayanta "Iyadunni Movement" da majalisar zartaswar NNPP ta jihar Ogun ƙarƙashin jagorancin Olaposi Sunday Oginni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinta, Kassim tace:

"Abu ne mai matuƙar haɗari ga burina na siyasa mu tunkari babban zaɓen 2023 da kai a rabe kamar yadda take faruwa a NNPP ta Ogun."
"Ba zai yuwu ina aiki don ci gaban jam'iyya ba yayin da wasu zasu maida hankali wajen yi mun zagon ƙasa. Buri na shine lashe zaɓe ba wai na yi sulhu da wata jam'iyya ba."
"Ina son dukkan mu anan mu yanke hukuncin ko zamu cigaba da abinda muka faro domin bana son kowa ya ji ba daɗi. Duk da masu kokarin rusa mu ba 'yan asalin Ogun bane."

Wane mataki suka ɗauka a taron?

Baki ɗaya magoya bayan yar takaran daga ƙananan hukumomi 20 dake faɗin Ogun suka cimma matsayar raba gari da NNPP, amma sun jaddada cewa kafarsu ƙafar Jackie Kassim, duk inda ta koma suna tare da ita.

Kara karanta wannan

2023: Ƙarin Matsala ga Atiku, Wani Shugaba a PDP da Ɗaruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Sun ayyana cewa daga ranar basu ba jam'iyyar NNPP kuma ba su fatan wani abu ya haɗa su alaƙa da jam'iyyar a jihar Ogun. Sun amince su kafa kwamitin da zai yi nazari kan jam'iyyar da zasu koma.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Wani Jigon Siyasa a Kano, Ya Koma Bayan Tinubu

Bashir Ahmad, Hadimin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari yace jam'iyya mai mulki ta ƙara karfi a mahaifarsa jihar Kano.

A cewarsa, Sakataren jam'iyyar Labour Party (LP) ya sauya sheka zuwa APC, ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel