Wasu Sunce Na Mutu, Sunce Na Janye, Amma Kwalelenku Ina Nan Lafiya: Tinubu

Wasu Sunce Na Mutu, Sunce Na Janye, Amma Kwalelenku Ina Nan Lafiya: Tinubu

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sak sabon bidiyo don nunawa yan Najeriya cewa shi fa yana cikin koshin lafiya
  • Dan takaran kujerar shugaban kasa na APC ya garzaya birnin Landan, kaar Birtaniya don hutawa
  • Ana rade-radin cewa Tinubu ya tafi Landan jinya ne na wani rashin lafiya da yake fama

Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi watsi da jita-jitan da ake cewa jinya ya tafi birnin Landan.

Tinubu ya saki sabon bidiyon da dan tsokaci a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba, 2022.

Bidiyon mai tsayin sakwanni bakwai kacal ya nuna Tnubu yana motsa jiki kan keken tafi da gidanka cikin dakinsa a Landan.

A jawabin da yayi, Tinubu yace:

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Yan Matan Kannywood 12 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Tinubu

"Wasu da dama sun ce na mutu; wasu sun ce na janye daga kamfen neman shugaban shugaban kasa."
"Amma kash! Gaskiyan magana shine ina da karfi ne, ina cikin koshin lafiya kuma shirye nike da bautawa yan Najeriya tun ranar farko."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel