Tinubu Ya Nada Gwamna Masari da Tsohon Gwamnan Sokoto a Muhimmin Muƙaman Kamfe
- Asiwaju Bola Tinubu ya naɗa gwamna Masari na Katsina da Sanata Wamakko a wasu mukaman tawagar kamfen APC
- Wannan na zuwa ne bayan ɗan takarar ya naɗa gwamna Mai Mala Buni da Yahaya Bello duk daga yankin arewa a tawagar
- Tuni dai INEC ta buɗe fagen dagar yaƙin neman zaben shugaban ƙasa, amma APC ta jinkirta kaddamar da tawagarta
Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya naɗa gwamna Aminu Masari na Katsina a matsayin mashawarci na musamman kan jagoranci na tawagar kamfe.
Premium Times tace Tinubu ya kuma naɗa tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma Sanata mai ci, Aliyu Wamakko a matsayin babban mashawarci kan ayyuka na musamman.
A wasikun naɗin da aka raba wa manema labarai ranar Lahadi a Abuja kuma ɗauke da sa hannun Tinubu, dukka jiga-jigan biyu zasu yi aiki ne a tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.
Wasikun sun yi bayanin cewa Masari da Wamakko sun samu nasarori masu ban sha'awa a siyasa kuma shugabanni ne abin koyi a matsayin gwamna da Sanata, sun dace da muƙaman.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasiƙar naɗin da aka aike wa gwamna Masari tace:
"Ta wannan takarda muna sanar da kai cewa an naɗa ka mai ba da shawari na musamman kan harkokin shugabanci da gwamnati a tawagar kamfen Tinubu/Shettima."
"Wannan naɗi ya dace kuma a kan lokaci duba da nasarorinka a siyasa da kuma shugabanci abin koyi da kake aiwatarwa a matsayin gwamna da kuma mamban jam'iyya."
"Mun ji daɗin jawo ka cikin tawagar kamfe kuma mun san zaka yi duk me yuwuwa don sauke nauyin da aka dora maka dai-dai kwarkwado."
A wasiƙar, Tinubu, ya nuna kwarin guiwar cewa Masari zai taimaka wajen gudanar da kamfe mai tsafta da zai kai APC ga nasara a zaɓen 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A wani labarin kuma Mun haɗa muku Jerin Rukunin Yan Kasuwa 6 da Liyafarsu Zata Ɗaga Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe Na 2023
Najeriya zata shaida manyan harkokin kamfe waɗanda ka iya taɓa tattalin arzikin kasa. A zaɓen da ya wuce 2019 an ƙayyade iyakar kudin da kowace jam'iyya zata iya kashe wa Biliyan ɗaya.
Amma a zaɓen 2023, masu dokoki sun sake nazari sun ɗaga kuɗin zuwa biliyan N5bn a kundin zaɓe 2022.
Asali: Legit.ng