Tinubu Ya Nada Aisha Buhari Matsayin Jagorar Mata A Kamfensa, Ba Sunan Matar Osinbajo

Tinubu Ya Nada Aisha Buhari Matsayin Jagorar Mata A Kamfensa, Ba Sunan Matar Osinbajo

  • Dan takaran shugaban kasan APC Bola Tinubu ya baiwa uwargidar shugaba Buhari babban mukami
  • Tun gabannin fara aiyyana yakin neman zabe a hukumanche dai jami'iyyu da dama suka fitar da kunshin tawagar yakin neman zabensu
  • Ko a bayabayanan ma dai an zargi jami'iyar APC da kin sanya Sunan Mataimakin Shugaban Kasa a cikin kunshin tawagar yakin neman zaben

Jam’iyya mai mulki a Nijeriya ta APC, ta sanar da nada Matar shugaban kasa Aisha Buhari a matsayin wadda zata jagoranci mata a kamfen din jami’iyyar na 2023, a yau asabar.

Kwamittin mai taken “Tawagar mata masu kamfen din Tinubu/shattema” ana sa ran uwargidan shugaban kasa itace zata zama shugabar din wannan tawagar.

Sauran wadanda zasu taka rawa a tawagar sun hada da Sanata Oluremi Tinubu, Sanata mai wakiltan Legas ta tsakiya a zauren majalisar dattawa a wa'adi na uku a majalisar dattawa kuma tsohuwar uwargidan tsohon gwamnan jihar Legas, Nana Shettima, tsohuwar uwargidan gwamnan jihar Borno kuma uwargidan dan takarar mataimakin shugaban kasa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

2023: Nasihar da Shugaba Buhari Ya Yi Wa Yan Takarar Shugaban Kasa 18 a Wurin Taron Abuja

Tawagar dai zasu yi aiki ne a matsayin Shugaba da Mataimakan Shugabanin tawagar kamfe a bangaren mata.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Rinsola Abiola, diyar marigayi Cif MKO Abiola, kuma jigo a jam’iyyar APC ta fitar, wadda ita ma mambace a cikin kwamitin yada labarai na gudanarwar tawagar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Aisha Buhari
Tinubu Ya Nada Uwargidar Shugaba Buhari Matsayin Jagorar Mata A Kamfensa
Asali: Depositphotos

Asabe Vilita Bashir, tsohuwar ‘yar majalisar wakilai daga Borno za ta kasance babbar mai kula da tawagar, yayin da Lauretta Onochie, wata fitacciyar a jam’iyyar APC kuma babbar mai taimaka wa fadar shugaban kasa za ta dafa mata.

Yayin da tawagar mata ta shiyyar Arewa maso Yamma zasu kasance karkashin jagorancin Dr Zainab Baugudu, matar gwamnan jihar Kebbi, yayin da Misis Falmata Zulum, uwargidan gwamnan jihar Borno, ita ce mai kula da yankin arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

2023: Nan Babu Dadewa Wike da Tawagarsa Zasu Koma Wurin Tinubu, 'Dan APC Yayi Hasashe

Hakazalika, Uwargidan Gwamnan Jihar Kwara, Olufolake Abdulrazaq, za ta hada kan matan a yankin Arewa ta Tsakiya, sannan Misis Sanwo-Olu, uwargidan Gwamnan Jihar Legas, za ta kula da yankin Kudu-maso-Yamma.

Uwargidan Gwamnan Jihar Imo, Chioma Ikeaka-Uzodinma, ita ma za ta hada kan yankin Kudu maso Gabas yayin da Linda Ayade, uwargidan Gwamnan Jihar Cross River, za ta jagoranci yakin neman zaben mata a Kudu maso Kudu.

Duk matan gwamnonin za su yi aiki a matsayin kodineta na jihohi a jihohin APC, yayin da aka zabi fitattun matan APC kamar su Florence Ajimobi, matar tsohon gwamnan jihar Oyo da Zainab Ibrahim, mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa da dai sauransu a jihohin da APC ce iko da su ba.

Babban Kwamitin gudanarwada tsare-tsare na karkashin jagorancin Hon. Wahab Alawiye-King, hamshakiyar yar siyasar Legas kuma makusanciyar Oluremi Tinubu.

Ita ma shugabar kwamitin aiyuka da dabaru ita ce Sanata Fatima Raji-Rasaki yayin da Sarafa Modele-Yusuf, kwararriyar mai yada labarai, ita ce shugabar kwamitin yada labarai da dabarun sadarwa.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

Kwamitin kudi da ayyuka na musamman zai kasance karkashin jagorancin tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Legas kuma babbar mataimakiyar shugaban kasa, Gimbiya Adejoke Orelope-Adefulire.

Kwamitin kirkira nishadi kuma yana da gogaggun membobi da suka hada da Allon Diva, Joke Silva, a matsayin shugaba, kuma ya hada da wasu mambobi kamar su Toyin Adegbola, Esther Wright, Rose Odika da Hadiza Kabara, da dai sauransu.

Hukumar tuntuba da wayar da kan jama’a tana da mambobi 944 ciki har da Hon. Tolulope Akande Sadipe, Hon. Rekiya Yahaya, Zainab Ikaz-Kassim, da sauransu.

Jerin kuma ya kunshi ‘yan sa kai da suka hada da Zahra Buhari, Hafsa Umar Shinkafi, Ahmed Indimi, Mairo Bulama Idris, Aisha Ahmed Jika da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel