Shirin 2023: Jam'iyyar PDP Ta Rasa Jigo da Wasu Daruruwan Mambobi Zuwa APC a Edo

Shirin 2023: Jam'iyyar PDP Ta Rasa Jigo da Wasu Daruruwan Mambobi Zuwa APC a Edo

  • Jigon jam'iyyar PDP a yankin ƙaramar Hukumar Ovia ta kudu-yamma, jihar Edo da ɗaruruwan mambobi sun koma APC
  • Hon. George Edokpolor, yace babu wani mutumi mai cikakken hankali a mazaɓar Ovia da zai ci gaba da zama a jam'iyyar PDP
  • Jam'iyyar APC ta tabbatar wa masu sauya shekar cewa sun zama ɗaya da kowane mamba a wurin wani taro ranar Asabar

Edo - Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP reshen gundumar Ugbogui, ƙaramar hukumar Ovia ta kudu maso yamma a jihar Edo, Hon. George Edokpolor, da ɗaruruwan magoya bayansa sun koma APC.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa masu sauya sheƙar sun tabbatar da matakin da suka ɗauka ne a wurin wani taro da ya gudana a Ugbogui ranar Asabar.

Manyan jam'iyyu biyu.
Shirin 2023: Jam'iyyar PDP Ta Rasa Jigo da Wasu Daruruwan Mambobi Zuwa APC a Edo Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Da yake jawabi a wurin, Hon Edokpolor, yace:

Kara karanta wannan

2023: Na Sadaukar da Rayuwata da Komai Ga Al'ummar Jihar Katsina, Ɗan Takarar APC Dikko

"Babu wani mai cikakken hankali a mazaɓar Ovia ta tarayya da zai ci gaba da zama a PDP idan aka yi la'akari da ayyukan da Hon Dennis Idahosa, mamba mai wakiltar mazaɓar a majalisar dokokin tarayya ke aiwatarwa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edokpolor yace Idahosa ya kawo gwamnati kusa da al'umma, inda a cewarsa, "Mista Dennis Idahosa ya nuna cewa matuƙar mutane suka yi zaɓin da ya dace, suna da damar da zasu yi murna."

Meyasa suka yanke koma wa APC?

"Wannan ne ya sa muka yanke shawarin mu tattara kayanmu daga PDP kana mu koma mu haɗa karfi domin sake tura Idahosa majalisar wakilan tarayya domin ta haka ne kaɗai mutane zasu ci gaba da shan romon shugabanci mai nagarta."

"Idahosa bai nemi dole sai ya wakilci mutanen yankin mazaɓar ba amma akwai bukatar mazauna Ovia su yaba wa ƙoƙarinsa ta hanyar sake tura shi Abuja ya cigaba da abinda ya fara," inji George Edokpolor.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Jita-Jitar Wani Gwamnan PDP Ya Jingine Atiku, Ya Goyi Bayan Obi a 2023

Akwai sauran aiki a gaba - Idahosa

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa masu sauya sheƙar sun samu tabbacin ba za'a nuna musu banbanci ba a sabuwar jam'iyyarsu APC.

Da yake jawabi, Idahosa, wanda ya yi amfani da taron wajen zayyana wasu nasarorin da ya cimma, yace akwai sauran aiki a gaba saboda watsin da aka yi da mazaɓar a baya.

Ɗan majalisar ya nanata cewa hakan zata faru ne kaɗai idan mutane sun sake amince wa tare da mara masa baya a babban zaɓen 2023.

A wani labarin kuma dalilin Da Yasa Dole 'Yan Arewa Su Watsar da Atiku, Su Zabi Bola Tinubu a Babban Zaben 2023

Mai neman zama Sanatan Kaduna ta tsakiya, Muhammad Dattijo, yace 'yan Arewa ba su da zabin da ya wuce Tinubu/Shettima a 2023.

Da yake tsokaci kan irin wanda da ya dace ya gaji Buhari, Dattijo yace yan arewa na bukatar mutumin dake ƙaunar yankinsu.

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Wani Jigon Siyasa a Kano, Ya Koma Bayan Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262